Kungiyar dalibai ta NANS ta kai kukan ta ga Sheikh Gumi da Buhari kan sace dalibai
- Kungiyar dalibai a Najeriya ta bayyana bukatar ayyana 'yan bindiga a matsayin 'yan ta'adda
- Wannan na fito wa ne daga bakin shugaban NANS a ranar Lahadi 8 ga watan Agustan 2021
- Ya yi kira da gwamnati ta inganta lamarin tsaro a dukkan makarantun dake fadin Najeriya
Ekiti - Kungiyar Daliban Najeriya ta kasa (NANS) ta yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya ayyana barayin da ke sace dalibai a yankin arewacin kasar a matsayin ‘yan ta’adda.
Daily Trust ta ruwaito cewa shugaban NANS na kasa, Sunday Asefon, ya yi wannan kiran ne a madadin kungiyar a ranar Lahadi, 8 ga watan Agusta, a Ado-Ekiti, jihar Ekiti.
Legit.ng ta tattaro cewa Asefon ya ce duk wanda ke da halin yin garkuwa da kashe dalibai to a bayyana shi a matsayin dan ta'adda kawai.
Ya yi Allah wadai da rufe wasu makarantu a wasu sassan arewacin kasar saboda karuwar satar dalibai, Nigerian Tribune ta kuma bayyana.
NANS ta gana da Sheikh Gumi
A halin da ake ciki, Asefon ya kuma bayyana cewa NANS ta gana da shahararren malamin addinin Islama, Sheikh Ahmed Gumi, kan halin da ake ciki na sace dalibai.
Ya ce an bukaci malamin addinin Islama da ya fada wa 'yan bindigar da su guji makarantun gwamnati da 'ya'yan talakawa ke karatu.
Sheikh Gumi wanda ke iya kokarinsa don dakatar da 'yan bindiga daga kara aikata munanan ayyuka yakan bayyana bukatar gwamnati ta tattauna da 'yan bindigan.
Ya kamata gwamnati ta inganta tsaro
Asefon ya kuma yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta karfafa tsaro a makarantu, lura da cewa ya kamata dalibai su iya zuwa makaranta ba tare da fargabar rashin tsaro ba.
A cewarsa:
“Ya kamata gwamnati ta karfafa tsaro a makarantu. Imanin mu ne cewa yakamata ɗalibai su tafi makarantu tare da tabbacin za su sami tsaro.
"Ina kira ga gwamnatin tarayya da ta ayyana wadannan barayin da ke sace dalibai a arewa maso yamma da arewa ta tsakiya a matsayin 'yan ta'adda."
Yadda aka cafke matashi mai shekaru 16 da ke satar shanu da garkuwa da mutane
A wani labarin, Rundunar ‘yan sandan jihar Oyo ta cafke wani barawon shanu mai shekaru 16, Umaru Muhammed, kan garkuwa da mutane a Ibadan.
Muhammad ya amsa cewa yana cikin gungun masu garkuwa da mutane yayin da yake amsa tambayoyi a hedkwatar rundunar, Eleyele, Ibadan, Daily Trust ta ruwaito.
A cewarsa,wanda suka yi awon gaba dashi na karshe sun rude shi da ya zo ya sayi shanu ne a kauyen Akinyele, Karamar Hukumar Akinyele a Ibadan, babban birnin jihar Oyo.
Wanda ake zargin da ya amsa cewa shi barawon shanu ne ya ce wasu abokan aikinsa da a yanzu suke nemansa sun ce ya kira mutane su zo su sayi shanu a wurinsa.
Asali: Legit.ng