‘Yan bindiga sun kashe wani bawan Allah, sun nemi a biya miliyan N50 kudin fansar mata da ‘yarsa da suka sace
- Wasu da ake zaton masu garkuwa da mutane ne sun kai farmaki kan wasu iyalai a titin Ewu – Ayetoro Ekiti a jihar Ekiti
- An tattaro cewa maharan sun halaka mai gidan sannan suka yi garkuwa da mata da 'yarsa
- A yanzu haka an ce sun tuntubi 'yan uwansu inda suka nemi a biya naira miliyan 50 kafin su sake su
Ekiti - Wasu ‘yan bindiga a yammacin ranar Juma’a sun kai hari kan wasu iyalai da ke tafiya a kan titin Ewu – Ayetoro Ekiti a jihar Ekiti, inda suka kashe wani mutum tare da yin garkuwa da matarsa da diyarsa.
An tattaro cewa wadanda abin ya rutsa da su sun je jihar ne domin halartan wani jana'iza a Ewu Ekiti kuma an far masu yayin da suke tuki akan hanyar.
Wata majiya ta ce harbe-harben da maharan suka yi ya sa direban motar ya rasa yadda zai yi sannan ya kutsa cikin daji, jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Ya ce an harbe daya daga cikin mutanen da ke cikin motar inda ya mutu a nan take.
Majiyar ta kara da cewa masu garkuwa da mutanen sun tuntubi iyalan kuma sun bukaci kudin fansa na naira miliyan hamsin don kubutar da matar da diyarta.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Ekiti, Sunday Abutu, ya tabbatar da faruwar lamarin sannan ya ce an cafke mutum daya da ake zargi.
Abutu ya ce bisa labarin da aka samu, 'yan sanda sun cafke wani mai suna Akinola Femi, wanda ake zargin yana daya daga cikin masu yi wa masu garkuwa da mutane leken asiri a yankin Ido/Osi na jihar.
Ya ce:
"A halin yanzu ana yi wa Femi tambayoyi kuma ana bincike don ci gaba da samun bayanai."
Da yake yiwa manema labarai karin haske kan abin da ya faru a Ado-Ekiti a ranar Asabar, Erinle, wanda ya kasance dan majalisar dokokin Ekiti daga 2011 zuwa 2015, ya tabbatar da bukatar kudin fansa daga masu garkuwar.
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Erinle ya ce wadanda abin ya rutsa da su abokai ne na danginsa.
'Yan bindiga sun yi garkuwa da kwamishinan Neja a garinsa
A wani labari na daban, mun ji cewa 'yan bindiga dauke da makamai sun yi garkuwa da kwamishinan yada labarai na jihar Neja, Alhaji Sani Idris.
Jaridar The Nation ta rahoto cewa Alhaji Ahmed Ibrahim Matane, sakataren gwamnatin Neja ne ya sanar da wannan labari mai tayar da hankali.
Asali: Legit.ng