Gwamna ya rushe gidan da masu garkuwa suka ajiye matar kwamishina da direbanta a Benue

Gwamna ya rushe gidan da masu garkuwa suka ajiye matar kwamishina da direbanta a Benue

  • Gwamna Ortom ya bada umurnin a rushe gidan da aka yi amfani da shi wurin ajiye matar kwamishina da aka direbanta da aka sace
  • Gwamnan na jihar Benue ya bada umurnin ne bayan yan sanda sun ceto wadanda aka sacen a ranar Litinin 2 ga watan Agusta
  • Ortom ya yi bayanin cewa an dauki matakin ne bisa tanadin dokar jihar Benue da ta shafi garkuwa da mutane

Makurdi, Jihar Benue - Gwamnan jihar Benue ya bada umurnin a rushe gidan da yan sanda suka kashe mutane uku da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sannan suka ceto matar kwamishina da direbanta.

Legit.ng a baya ya ruwaito cewa jami'an tsaron Operation Zenda a ranar Litinin, 2 ga watan Agusta sun kashe masu garkuwa da mutane biyu suka ceto Mrs Ann Unnege, matar kwamishinan kasa da sifiyo.

Gwamna ya rushe gidan da masu garkuwa suka ajiye matar kwamishina da direbanta a Benue
Gwamna ya rushe gidan da masu garkuwa suka ajiye matar kwamishina da direbanta a Benue. Hoto: Ukan Kurugh
Asali: Facebook

The Punch ta ruwaito cewa Gwamna Samuel Ortom wanda daga bisani a ziyarci hedkwatar yan sanda a Makurdi ya bada umurnin a rushe gidan da aka ajiye wadanda aka yi garkuwan da su.

Kara karanta wannan

Babban Kamu: FBI ta kwamuso wasu 'yan Najeriya da ke damfara a kasar Amurka

Ya yi bayanin cewa hakan ya yi dai-dai da tanadin dokar hana satar mutane, garkuwa, kungiyoyin asiri da sauransu a Benue.

Legit.ng ta gano cewa ginin yana unguwar BIPC Quarters, ne a Nyinma Layout, Makurdi kuma an rushe ginin bayan umurnin gwamnan.

An bukaci masu gidajen haya su rika bincike kan mutanen da za su bawa gidajensu haya

Da ya ke magana kan lamarin, mashawarcin Gwamna Ortom kan tsaro Kwanel Paul Hemba (mai murabus) ya bukaci masu gidaje su rika bincike kan mutane kafin su basu gidajensu haya.

Hemba ya ce za a kwace izinin gini a filin da aka gina gidan kamar yadda dokar jihar ta tanada.

Gwamna Ortom ya yabawa yan sanda, yana mai cewa jarumtar da suka yi zai zama darasi ga sauran bata gari cewa jihar Benue ba matattaran masu laifi bane.

Yadda yan bindigan suka sace matar kwamishinan da direbanta a Benue

Tunda farko, mun kawo muku rahoton cewa Ann Unenge, matar kwamishinan filaye na Benuwai, ta shiga hannun wasu masu garkuwa da mutane a Makurdi, babban birnin jihar.

Kara karanta wannan

Yanzu: Rikici ya barke tsakanin dan Shi'a da mazauna a Kano, ya jawo kone-kone

Wani dan uwan ​​Unenge ya fadawa jaridar The Nation cewa an sace ta ne da yammacin ranar Alhamis, 29 ga watan Yuli, da karfe 6:00 na yamma.

An tattaro cewa an yi garkuwa da matar yayin da miyagun suka kuma sace sabuwar motarta kirar Toyota Highlander wacce take tukawa a ranar da abun ya faru.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel