Rikici ya barke tsakanin jama'an gari da yan Shi'a a jihar Kano

Rikici ya barke tsakanin jama'an gari da yan Shi'a a jihar Kano

  • An samu sabani tsakanin yan Shi'a da yan unguwar Dorayi
  • Wasu yan Shi'a sun bayyana cewa yan Izalah ne suka kawo muku hari
  • Jami'an yan sanda sun damke akalla mutum huda

Kano - A ranar Litinin, an ruwaito barkewar rikici tsakanin jama'an yankin Dorayi Babba a jihar Kano da mabiyar kungiyar IMN da aka fi sani da mabiyar akidar Shi'a.

Wannan rikici ya barke ne yayinda yan unguwar sukayi yunkurin hana yan Shi'an gudanar da taronsu 'Ghadeer' a unguwar.

Rahoton Premium Times ya bayyana cewa yan Shi'an sun shirya gudanar da taron ne a kan fili mallakin wani mutumi wanda shima dan Shi'a ne amma aka hanasu.

Majiyoyi a unguwar sun bayyana cewa dattawa a yankin sun bukaci mai filin ya sayar da filin saboda basu son yadda yan Shi'a ke taruwa a wajen.

Wani mazaunin unguwar, Bilyaminu Abubakar, ya bayyanawa PT cewa:

"Wasu dattawa sun bayyana cewa hankalinsu bai kwanta da yadda yan Shi'a ke taruwa a wajen ba. Mai filin yace N50,000,000 zai sayar da filin amma sunce N12,000,000 zasu iya bashi."

Kara karanta wannan

An Kama Mata Da Miji Da Suka Yi Ƙaryar Garkuwa Da Ƴarsu Don Su Samu Kuɗi Su Biya Bashin Banki Ta Suka Ci

Yace lokacin da wasu daga cikin yan Shi'an suka isa wajen don taron ranar Litinin, wasu matasa suka kalubalancesu, kawai sai aka cakume da rikici.

Rikici ya barke tsakanin jama'an gari da yan Shi'a a Kano
Rikici ya barke tsakanin jama'an gari da yan Shi'a a jihar Kano Hoto: PTimes
Asali: Facebook

Wani mai suna Aminu Miko yace:

"Mutan unguwar sun kona wata mota mallakin Saleh Haruna kurmus."

Ya kara da cewa mutane da dama sun jigata.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, Abdullahi Kiyawa, yace tuni an damke mutum hudu dake da hannu cikin rikicin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel