Da duminsa: Annobar Korona ta barke a sansanin NYSC na jihar Gombe

Da duminsa: Annobar Korona ta barke a sansanin NYSC na jihar Gombe

  • Daga jihar Gombe, annobar Korona ta shiga sansanin 'yan bautar kasa, ta harbu ga mutane 25
  • An garzaya dasu cibiyar killacewa a jihar don basu magunguna da kulawar da ta kamata
  • Gwamnatin jihar tuni ta samar da dukkan abubuwan da ake bukata da suka shafi tsaro da magani

Jihar Gombe - Akalla membobin bautar kasa 25, ciki har da mai shayarwa, suka kamu da cutar Korona a sansanin NYSC na jihar Gombe da ke Amada, Karamar Hukumar Akko.

Da yake tabbatar da lamarin a ranar Asabar a wata tattaunawa ta musamman, Kwamishinan Lafiya, Dakta Habu Dahiru, ya ce an yi wa masu yi mutane 25 gwaji a cikin kwanaki ukun da suka gabata, Punch ta ruwaito.

Ya kara da cewa an tura su zuwa cibiyar killacewa mallakar jihar a cibiyar cututtuka na Idris Mohammed da ke Kwadon.

Da duminsa: Annobar Korona ta barke a sansanin NYSC na jihar Gombe
Annobar Korona | Hoto: nairametric.com
Asali: UGC

Ya ce:

“Daga cikin 1,291 da aka gwada ta yin amfani da Polymerase Chain Reaction, mutane 25 sun kasance sun kamu, kuma daya daga ciki uwa ce mai shayarwa."

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: EFCC ta kama Saraki kan sabbin zarge-zargen cin hanci da rashawa

Ya kuma kara da cewa, a halin yanzu an dasa 'yan sanda a cibiyar killacewar don tabbatar da tsaro har zuwa lokacin da za su warke.

Hakazalika, a cewarsa, an tanadi abinci da magunguna ga mambobin bautar kasar tare da kyakkyawan tsaro.

'Yan wane yanki ne suka kawo Korona sansanin?

Dr Dahiru ya kara da cewa galibin wadanda abin ya shafa sun fito ne daga jihohin da aka samu bullar sabuwar nau'in Korona ta Delta, Daily Trust ta ruwaito.

Kwamishinan, wanda shi ma shugaban tsarin gudanarwa ne na Management System (IMS) a jihar, ya ce wadanda abin ya shafa za su kasance a killace na tsawon mako guda, sanan za a gudanar da wani gwajin a kan su.

Ya yi kira ga jama'a da suci gaba da lura da ka'idojin Korona na kiyaye tazara, amfani da takunkumin fuska da kuma wanke hannaye da sabulu da ruwa da sinadarin kashe cututtuka.

Kara karanta wannan

El-Zakzaky da Matarsa na shirin fita daga Najeriya don ganin Likita

Rikicin Kabilanci: Gwamnatin Gombe ta sanya dokar ta-baci a wasu yankuna 7

Har ila yau a jihar ta Gombe, a ranar Talatar da ta gabata ne Gwamnatin Jihar Gombe ta sanya dokar hana fita ta sa’o’i 24 a kan wasu al’ummu bakwai da ke karamar hukumar Balanga ta jihar.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Ismaila Uba-Misilli, Darakta-Janar na harkokin yada labarai, na gidan gwamnatin Gombe ya fitar.

Mista Uba-Misilli ya ce Sakataren Gwamnatin Jihar, Ibrahim Njodi ne ya bayyana hakan.

An ruwaito Mista Njodi yana cewa matakin ya biyo bayan sake barkewar rikici tsakanin kabilun Lunguda da Waja a cikin al'ummomin a safiyar Talata 27 ga watan Yuli, VON ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.