Bayan dakatar da Abba Kyari, IGP ya gargadi sauran jam'ian 'yan sandan Najeriya

Bayan dakatar da Abba Kyari, IGP ya gargadi sauran jam'ian 'yan sandan Najeriya

  • Bayan dakatar da Abba Kyari, IGP ya gargadi rundunar 'yan sandan Najeriya kan kare mutuncinsu
  • IGP ya bukaci dukkan jami'an 'yan sanda da su tabbatar suna da goyon bayan al'ummar kasar
  • Ya bayyana haka ne a wani taro a jihar Legas a jiya Lahadi 1 ga watan Agustan wannan shekarar

Lagos - A yayin da aka dakatar da shugaban rundunar IRT, Abba Kyari, Sufeto-Janar na 'yan sanda (IGP) Alkali Baba Usman ya gargadi dukkan jami'an da kada su kuskura su zubar da mutuncinsu a idon jama'a.

Nigerian Tribune ta ruwaito cewa Usman, ya yi wannan gargadin ne yayin kaddamar da ayyukan miliyoyin nairori da Olusoji Akinbayo, kwamandan runduna ta “B”, Apapa ya yi.

Shugaban 'yan sandan wanda ya samu wakilcin Johnson Kokumo, Mataimakin Sufeto Janar na 'yan sanda (AIG) a sashen runduna ta 2 da ke jihar Legas, ya bayyana hakan ne a karshen mako.

Ya ce da zarar jami'i ya rasa goyon bayan jama'a to bai da wani dalilin da zai sadaukar da mutuncin ofishin sa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Zamfara ta nemi a dauki tsatsauran mataki kan masu safarar mutane da sauransu

Biyo bayan dakatar Abba Kyari, IGP ya gargadi sauran jam'ian 'yan sandan Najeriya
IGP Usman Baba Alkali | Hoto: businessday.ng
Asali: UGC

A cewar Usman, daya daga cikin hanyoyi mafi sauki don ci gaba da tallafawa jama'a shine jami'an su tabbatar da cewa ba su zubar da kyakykyawan mutuncinsu ba, The Sun ta kara da cewa.

Yayin da yake lura da cewa rawar da Akinbayo ya taka wanda yanzu aka kara masa girma zuwa mukamin mataimakin kwamishinan 'yan sanda ya cancanci yabo da koyi, IGP ya bayyana cewa babban jami'in ya nuna kwarewar aiki.

Me yasa aka dakatar da Abba Kyari?

Hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda ta dakatar da Abba Kyari, mataimakin kwamishinan 'yan sanda kuma shugaban rundunar IRT daga gudanar da ayyuka da ayyukan ofishinsa, Vanguard ta ruwaito.

Wata sanarwa da Ikechukwu Ani, Babban jami'in Hulda da Jama'a ya ce:

"Dakatarwar Abba Kyari ta fara aiki daga ranar Asabar, 31 ga Yuli, 2021 kuma za ta ci gaba da jiran sakamakon bincike dangane da tuhumar da Ofishin Binciken Tarayyar Amurka ya yi.

Kara karanta wannan

Abubuwa 10 Da Ta Yi Wu Baka Sani Ba Game Da DCP Abba Kyari

“Hukumar ta kuma umarci Sufeto Janar na 'yan sanda da ya ba ta bayanai kan ci gaba kan lamarin don daukar matakin da ya dace.

Matasan Arewa sun yi kakkausan martani kan kotun Amurka kan batun Abba Kyari

A wani labarin, Kungiyar Arewa Youth Consultative Forum (AYCF) ta yi kaca-kaca da Kotun Amurka da ke zargin Abba Kyari da cin hanci tare da bayar da umarnin cafke jami'in.

Sanarwar da shugaban AYCF na kasa, Yerima Shettima ya aikewa Legit.ng, ta bayyana umarnin a matsayin yunkurin tozarta jami'in dan sandan a cikin mahaifarsa kuma kasarsa mai zaman kanta.

Shettima, ya kuma yi gargadin cewa a tabbata abubu abin da zai faru da Kyari, inda ya bayyana matakin da FBI ta dauka a matsayin "abin da ba za a amince da shi ba, cin fuska ga 'yan kasarmu da izgili ga daya daga cikin manyan jami'anmu masu aiki tukuru."

Kara karanta wannan

‘Yan sanda sun yi ram da wasu maza biyar da ke lalata da junansu a Kano

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

iiq_pixel