Wannan juyin mulki ne, Gwamna Wike ya koka kan zargin makirci a majalisar dokokin kasa

Wannan juyin mulki ne, Gwamna Wike ya koka kan zargin makirci a majalisar dokokin kasa

  • Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya bayyana kuskuren 'yan majalisar dokokin kasar da suka kada kuri'ar kin amincewa da sakamakon zabe ta na’ura
  • Dan siyasan ya ba da shawarar cewa akwai bukatar watsa sakamakon zabe ta na’ura don yin sahihin zabe
  • Wasu ‘yan majalisun tarayya sun sha suka mai tsanani daga mambobin jam’iyyar adawa kan batun

Fatakwal, jihar Ribas - Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya zargi 'yan majalisar dokokin kasar da suka kada kuri'ar kin amincewa da tura sakamakon zabe ta na’ura da shirya makarkashiyar juyin mulki ga al'ummar Najeriya.

Gwamnan ya yi wannan zargin ne ta shafinsa na sada zumunta na Facebook a ranar Talata, 3 ga watan Agusta.

Wannan juyin mulki ne, Gwamna Wike ya koka kan zargin makirci a majalisar dokokin kasa
Wike yace membobin NASS sun shirya juyin mulki ta hanyar kin amincewa da watsa sakamakon zabe ta na’ura Hoto: Gov Nyesom Ezenwo Wike - CON
Asali: Facebook

Ya ce ya kamata 'yan majalisar tarayya da ba su goyi bayan watsa sakamakon zabe ta na’ura ba su ji kunyar kansu.

Wike ya bayyana su a matsayin makiyan kasar.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Ina Goyon Bayan a Baiwa Yan Kudu Mulkin Najeriya a 2023, Gwamnan Arewa

Gwamnan ya ce akwai shakku kan kudurin Shugaba Buhari na gudanar da sahihin zabe tun lokacin da jam’iyyarsa ta ki amincewa da tantance sakamakon zabe ta na’ura.

Wike ya ce:

"Shugaban kasa ba zai iya gaya mana cewa da gaske yana son gudanar da sahihin zabe, na gaskiya da amana ba idan shi/jam'iyyarsa ta ki amincewa da gaskiya da watsa sakamakon zabe ta na’ura.
"Wadanda suka kada kuri'ar kin amincewa da watsa sakamakon zabe ta na’ura yakamata su ji kunyan kansu saboda su makiyan kasar ne.
"Juyin mulki ne akan mutane, Majalisar kasa ta yi shirin yi wa ‘yan Najeriya juyin mulki.
''Idan 'yan Najeriya suna da tunani babu wanda ya kamata ya iya komawa mazabarsa cikin wadanda suka kada kuri'ar kin amincewa da watsa sakamakon zabe ta na’ura."

A karshe gwamnonin PDP sun yi martani, sun bayyana matsayinsu kan tura sakamakon zabe ta na’ura

Kara karanta wannan

Hukumar hisbah ta damke wani mai kyamis da ke lalata da mata a Kano

A baya mun kawo cewa yayin da ake takaddama kan kin amincewa da watsa sakamakon zabe ta na'ura da majalisar dattawa ta yi, kungiyar gwamnonin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta mayar da martani a karshe.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, gwamnonin, sun nace cewa dole ne Majalisar Dokoki ta Kasa ta amince da yada sakamakon zaben ta na'ura.

Asali: Legit.ng

Online view pixel