Zaben 2023: Ina Goyon Bayan a Baiwa Yan Kudu Mulkin Najeriya a 2023, Gwamnan Arewa

Zaben 2023: Ina Goyon Bayan a Baiwa Yan Kudu Mulkin Najeriya a 2023, Gwamnan Arewa

  • Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya bayyana ra'ayinsa na tsarin mulkin karba-karba
  • Gwamnan yace shi kan shi wannan tsarin ne a Nasarawa ya kai shi ga zama gwamna
  • Sai dai manyan jam'iyyun ƙasar nan biyu APC mai mulki da PDP ba su ɗauki matsaya ba kan wannan lamarin

Nasarawa:- Yayin da zaɓen 2023 ke kara gabatowa, gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya yi kira da aiwatar da mulkin karba-karba domin kowane yanki ya amfana.

Gwamnan ya yi wannan kira ne ranar Litinin a wata tattaunawa da kafar watsa labarai ta channels tv cikin shirin su na 'Sunrise Daily'

Wannan na zuwa ne yayin da ake samun karuwar neman a kai wa kudanci mulkin kasar nan a babban zaɓen dake tafe.

Gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule
Zaben 2023: Ina Goyon Bayan a Baiwa Yan Kudu Mulkin Najeriya a 2023, Gwamnan Arewa Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Gwamna Sule yace:

"Na amince da tsarin mulkin karba-karba, na yi matukar amincewa da hakan ɗari bisa dari. Amma wannan hange na ne bawai na gwamnonin jam'iyyar APC ba."

Kara karanta wannan

Fadar Shugaban Kasa Ta Maida Martani Kan Zargin da Sule Lamido Ya Jefa Wa Buhari

Meyasa gwamna Sule ya faɗi haka?

Gwamnan ya bayyana cewa shi kanshi tsarin mulkin karba-karba ne ya kaishi ga zama gwamnan jihar Nasarawa.

Sule ya kara da cewa ya kamata a zaɓo mutumin kwarai wanda aka amince da shi ya zama shugaban ƙasar nan daga wannan yanki.

Shin manyan jam'iyyu sun yarda da tsarin?

Har zuwa yanzun, jam'iyyar APC mai mulki da babbar mai adawa PDP ba su bayyana matsayarsu ba game da wannan tsarin na karba-karba.

Yankin kudu-gabas, kudu-yamma da kudu-kudu sune suka haɗa gaba ɗaya kudancin Najeriya.

Kudu-yamma sun samar da Olusegun Obasanjo, wanda ya mulki kasar nan na tsawon zango biyu daga 1999-2007.

Kudu-kudu sun samar da Goodluck Jonathan, wanda ya yi mulki na tsawon shekara biyar.

A wani labarin kuma Yan Bindiga Sun Kai Hari Kauyukan Kaduna, Sun Hallaka Aƙalla Mutum 18

Aƙalla mutum 18 ne suka rasa rayukansu ciki har da ɗan sanda a wani harin da yan ta'adda suka kai kauyuka biyar dake yankin Chawai, karamar hukumar Kauru, jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Zamfara ta nemi a dauki tsatsauran mataki kan masu safarar mutane da sauransu

Ƙauyukan da lamarin ya shafa sun haɗa da Kigom, Kikoba, Kishisho da kuma Unguwan Magaji, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel