Yanzu Yanzu: A karshe gwamnonin PDP sun yi martani, sun bayyana matsayinsu kan tura sakamakon zabe ta na’ura

Yanzu Yanzu: A karshe gwamnonin PDP sun yi martani, sun bayyana matsayinsu kan tura sakamakon zabe ta na’ura

  • Gwamnonin da aka zaba a karkashin jam'iyyar PDP sun yi Allah wadai da kin amincewa da watsa sakamakon zabe ta na'ura
  • Mambobin majalisar dattawa sun ba da sharadi don watsa sakamakon zaben ta na'ura
  • Aminu Tambuwal, gwamnan jihar Sakkwato, wanda ya yi magana a madadin takwarorinsa, ya ce akwai bukatar a gudanar da zabe na gaskiya da adalci a kasar

A yayin da ake takaddama kan kin amincewa da watsa sakamakon zabe ta na'ura da majalisar dattawa ta yi, kungiyar gwamnonin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta mayar da martani a karshe.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, gwamnonin, sun nace cewa dole ne Majalisar Dokoki ta Kasa ta amince da yada sakamakon zaben ta na'ura.

Yanzu Yanzu: Daga karshe gwamnonin PDP sun yi martani, su bayanna matsayinsu kan tura sakamakon zabe ta na’ura
Gwamnonin PDP sun ce ba gudu ba ja da baya kan tura sakamakon zabe ta na’ura Hoto: Official PDP.
Asali: Facebook

Legit.ng ta tattaro cewa majalisar dokokin kasar tayi watsi da bukatar yayin zaman majalisar kan kudurin dokar zabe (Kwaskwarima).

Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, ya ce samar da sakamakon zaben ta na'ura ba mai yiwu bane tukuna a kasar.

Kara karanta wannan

Gwamnonin PDP: Buhari ya mayar da fadar shugaban kasa sakateriyar APC

A martaninsu, gwamnonin PDP sun dage kan lallai sai Majalisar Kasa ta samar da dokoki don ganin yiwuwar hakan.

A wata sanarwa mai kunshe da sharudda goma a karshen taronta a Bauchi, babban birnin jihar Bauchi a ranar Litinin, 26 ga watan Yuli, shugaban kungiyar gwamnonin, Waziri Tambuwa ya ce gwamnonin sun gano bukatar yin zabe na gaskiya da adalci a kasar.

Tambuwal ya kuma yi kira ga Majalisar Dokoki ta kasa da ta nemi a gabatar da sakamakon zaben ta hanyar amfani da na’ura a bangaren shari’ar kasar.

Ya ce:

"A kan Kwaskwarimar Dokar Zabe, Gwamnonin sun gano bukatar yin zabe na gaskiya da adalci a cikin kasar kuma sun yi kira ga Majalisar Dokoki ta kasa da ta nemi a samar da sakamakon zaben ta na'ura a kasar.”

Gwamnan ya kuma nemi Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da ta tura fasahohin da suka dace don tabbatar da kuri’un dukkan ‘yan Najeriya.

Kara karanta wannan

Dalilin da yasa farashin kayan Masarufi yayi tashin gwauron zabi, Shugaba Buhari

Gwamna Ya Caccaki Sanatocin APC, Ya Fadi Munafuncin da Suke Shiryawa a Zaben 2023

A wani labarin kuma, gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom, ya zargi cewa mambobin jam'iyyar APC sun yi fatali da dokar tura sakamakon zaɓe ta na'ura ne saboda suna ƙulla-ƙullar maguɗin zaɓe a 2023, kamar yadda leadership ta ruwaito.

Gwamna Ortom, ya faɗi haka ne yayin wata fira da manema labarai, ya yi gargaɗin cewa jiharsa ta PDP ce, kuma duk wanda ke shirin maguɗin zaɓe a 2023 to ya sake tunani.

A cewar gwamnan, masu zaɓe a jihar Benuwai suna da ilimi kuma sun san abinda suke yi, sannan a shirye suke a kowane lokaci su bada kariya ga ƙiri'unsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel