Allah ya yi wa tsohon ministan Najeriya rasuwa bayan doguwar jinya

Allah ya yi wa tsohon ministan Najeriya rasuwa bayan doguwar jinya

  • Gwamnatin jihar Zamfara ta tabbatar da mutuwar tsohon ministan noma, Malami Buwai
  • Gwamna Bello Matawalle ya bayyana kaduwarsa kan rasuwar dattijon dan majalisar wanda ya rasu a babban birnin jihar Zamfara
  • Ba a bayyana ciwon da ya yi sanadiyyar mutuwar Malami Buwai ba a lokacin kawo wannan rahoton

Tsohon ministan noma, Malami Buwai, ya rasu bayan doguwar jinya.

TVC News ta rahoto cewa Buwai ya mutu a ranar Litinin, 2 ga watan Agusta, a Gusau, babbar birnin jihar Zamfara.

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya bayyana rasuwar tsohon ministan a matsayin babban rashi ba ga jihar Zamfara kadai ba har ma ga ƙasar baki ɗaya.

Allah ya yi wa tsohon ministan Najeriya rasuwa bayan doguwar jinya
Allah ya yi wa tsohon ministan noma, Malami Buwai ya rasu a jihar Zamfara Hoto: Ibrahim Yusuf Dan Hausa
Asali: Facebook

A cewarsa, Buwai ya ba da gudummawa sosai ga ci gaban Zamfara musamman wajen taimakon marasa galihu.

Matawalle ya roki Allah da ya gafarta kurakuran marigayi ministan sannan ya baiwa iyalansa karfin gwiwa na jure rashin.

Gidan Rediyon Najeriya Kaduna ya ruwaito cewa an binne marigayin a makabartar Gusau bayan sallar jana’izar da babban limamin masarautar Gusau, Liman Dan-Alhaji Sambo ya jagoranta.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Kotu Ta Dage Sauraron Karar Hadiman Sunday Igboho, Ta Fadi Dalili

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Muhammad Matawalle, da manyan jami’an gwamnati sun halarci jana’izarsa.

Manyan Masu Fada Aji Na Arewa Ke da Alhakin Ayyukan Yan Bindiga a Arewa, Matawalle Ya Fallasa

A wani labari na daban, gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, a ranar Lahadi, yace shugabannin arewa ke da alhakin matsalar tsaron da ya mamaye yankin.

Matawalle ya yi wannan hangen ne yayin da yake gabatar da wata takarda mai taken "Yaki da yan bindiga a yankin arewa maso yamma: Ƙalubale da hanyar warware su" a wurin taron ƙaddamar da sabbin shugabannin ƙungiyar marubutan arewa a Kaduna.

Yace shugabannin arewa suke da alhakin yanayin da yankin ke ciki, wanda ya haɗa da aikata manyan laifuka kamar fyaɗe, kisan mata da ƙananan yara, sace mutane, fashi da makami da sauran manyan laifukan da suka mamaye yankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng