Yanzu-Yanzu: Hukumar DSS Ta Gurfanar da Hadiman Sunday Igboho a Gaban Kotu

Yanzu-Yanzu: Hukumar DSS Ta Gurfanar da Hadiman Sunday Igboho a Gaban Kotu

  • Kotu ta dage sauraton karar makusantan Sunday Igboho, har zuwa Laraba 4 ga watan Agusta
  • Wannan ya faru ne saboda wasu matsaloli da aka samu zaman yau dangane da sunayen mutanen
  • Hukumar DSS ta gabatar da mutun takwas daga cikin 12 da ake tsammanin suna hannunta

FCT Abuja:- Babbar kotun tarayya Abuja ta ɗage sauraron karar hadiman Sunday Igboho har zuwa ranar Laraba 4 ga watan Agusta, 2021.

Mai shari'a Egwuatu ya baiwa lauyan mutanen, Pelumi Olagbenjesi, damar wannan matakin domin ya gyara sunayen waɗanda yake karewa.

An samu wata yar hatsaniya a cikin kotun dangane da sunan mutum takwas da aka gabatar.

DSS ta gabatar da hadiman Sunday Igboho
Yanzu-Yanzu: Hukumar DSS Ta Gurfanar da Hadiman Sunday Igboho a Gaban Kotu Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Mutum nawa DSS ta gabatar gaban kotu?

Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta gabatar da hadiman Igboho 8 daga cikin 12 a gaban mai shari'a, Obiora Egwuatu, na babbar kotun tarayya dake zamanta a Abuja, kamar yadda channels tv ta ruwaito.

Punch ta ruwaito cewa Da farko kotun da dakatar da sauraron shari'ar saboda rashin halartar lauyan DSS amma daga baya lauyan ya iso.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Yan Bindiga Sun Mamaye Wasu Kauyukan Filato, Sun Kashe Mutane Tare da Kona Gidaje da Dama

A wani labarin kuma Fadar Shugaban Kasa Ta Maida Martani Kan Zargin da Sule Lamido Ya Jefa Wa Buhari

Kakakin shugaban ƙasa, Malam Garba Shehu, ya ƙalubalanci tsohon gwamna Sule Lamido, ya fito ya bayyana yadda Saminu Turaki ya sallama masa tikitin takarar gwamna a 2007.

Lamido ya yi Allah wadai da karbar da Buhari yakewa gwamnoni da yan majalisu a fadar shugaban ƙasa idan suka sauya sheka zuwa APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel