Hotunan ango da yayi wuff da zuka-zukan amare 4 a rana daya sun janyo cece-kuce

Hotunan ango da yayi wuff da zuka-zukan amare 4 a rana daya sun janyo cece-kuce

  • Wani mashahurin dan kasuwa a kasar Gabon ya zama jan gwarzo bayan ya tada kura a kafafen sada zumunta
  • An ga hotunan dan kasuwan ya aura mata hudu reras a rana daya a wani biki da aka yi lokaci daya
  • An gano sunan matan da aka aura a rana daya da Madeleine Nguema, Prisca Nguema, Nicole Mboungou, Carene Sylvana Aboghet.

Libreville, Gabon - Wani shahararren dan kasuwa a kasar Gabon ya janyo cece-kuce a kafar sada zumuntar zamani bayan ya aura mata hudu a lokaci daya a Libreville.

Dan kasuwan mai suna Mesmine Abessole ya aura mata a wani mashahurin biki da aka yi a ranar Asabar, 31 ga watan Yulin 2021, TheCable ta ruwaito.

KU KARANTA: Bayan farmakin Kareto, sojoji sun kai samame maboyar Boko Haram a Gubio, sun yi barna

Hotunan mutumin da yayi wuff da mata hudu a rana daya sun janyo cece-kuce
Hotunan mutumin da yayi wuff da mata hudu a rana daya sun janyo cece-kuce. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Sunayen matan kamar yadda aka tattaro shine Madeleine Nguema, Prisca Nguema, Nicole Mboungou, Carene Sylvana Aboghet, TheCable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Cin amana: Yadda Shakikin aminin ma'aikacin banki ya sheke shi, ya birne shi a Yobe

An ga hotunan mutumin da matansa hudu sanye da fararen rigunan amare rike da fulawoyi. Hotunan sun cigaba da samun tsokaci tun bayan bayyanarsu a kafafen sada zumunta.

KU KARANTA: 'Yan Sanda Sun Sheke Fitaccen mai Satar Jama'a da ya Saci Mahaifinsa ya Karba N4m na Fansa

Hotunan mutumin da yayi wuff da mata hudu a rana daya sun janyo cece-kuce
Hotunan mutumin da yayi wuff da mata hudu a rana daya sun janyo cece-kuce. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Hotunan mutumin da yayi wuff da mata hudu a rana daya sun janyo cece-kuce
Hotunan mutumin da yayi wuff da mata hudu a rana daya sun janyo cece-kuce. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Hotunan mutumin da yayi wuff da mata hudu a rana daya sun janyo cece-kuce. Hoto daga thecable.ng
Hotunan mutumin da yayi wuff da mata hudu a rana daya sun janyo cece-kuce
Asali: UGC

Duk da ba wannan bane karo na farko da aka fara ganin namiji ya aura fiye da mace daya ba a lokaci daya.

A kwanakin baya an ji labarin wani dan kasuwa a garin Abuja da ya aura mata biyu a rana daya, lamarin da ya janyo cece-kuce daga jama'a.

Samari sun dinga jinjinawa angon yayin da mata masu yawa suke ganin ba zasu iya jure hakan ba.

Hotunan Ango Yusuf Buhari da amarya Zahra Bayero yayin wasan Polon bikinsu

Rahotannin da Legit.ng ta fara tattarowa shine na fara shagalin bikin da daya tilo na shugaban kasa, Yusuf Muhammadu Buhari da diyar sarkin Bichi, Alhaji Nasir Bayero.

Kara karanta wannan

Abubuwa 10 Da Ta Yi Wu Baka Sani Ba Game Da DCP Abba Kyari

Kamar yadda shafin @insidearewa ya wallafa a daren ranar Juma'a, an ga hotunan amarya Zarah Bayero tare da angonta Yusuf yayin da ake gasar kwallon Polon bikinsu.

Wannan alama ce ta yadda aka fara shagalin bikin a ranar Juma'a duk da za a yi asalin daurin auren a farkon watan Augusta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel