Hotunan Ango Yusuf Buhari da amarya Zahra Bayero yayin wasan Polon bikinsu
- A ranar Juma'a aka fara shagalin bikin auren Yusuf Buhari da Zarah Bayero
- An fara shagalin ne da wasan kwallon Polo wanda amarya da angon suka halarta
- An ga ango Yusuf sanye da rigar wasan yayin da amarya Zarah ta saka bakar riga
Kano - Rahotannin da Legit.ng ta fara tattarowa shine na fara shagalin bikin da daya tilo na shugaban kasa, Yusuf Muhammadu Buhari da diyar sarkin Bichi, Alhaji Nasir Bayero.
Kamar yadda shafin @insidearewa ya wallafa a daren ranar Juma'a, an ga hotunan amarya Zarah Bayero tare da angonta Yusuf yayin da ake gasar kwallon Polon bikinsu.
Wannan alama ce ta yadda aka fara shagalin bikin a ranar Juma'a duk da za a yi asalin daurin auren a farkon watan Augusta.
KU KARANTA: Gara in dinga samun N5 a Najeriya a kan in fita kasar waje: Budurwa ta bada labarin wahalarta a kasar waje
An Yanke Wa Jagoran Waɗanda Ke Sace Yaran Kano Su Sayar Da Su a Kudu Ɗaurin Shekaru 104 Tare Da Tarar Kuɗi
Gwamnoni, ministoci da jiga-jigan gwamnati ne suka je neman aure
A cikin watan Yuli ne tawagar gwamnoni, ministoci da kuma jiga-jigan 'yan siyasa wadanda suka samu jagorancin Gwamna Badaru na jihar Jigawa suka dira a birnin Dabo domin nemawa Yusuf Muhammadu Buhari aure Gimbiya Zarah Bayero.
An kai lefen Zarah Bayero a watan Yuli
Har ila yau, duk a cikin watan ne mata suka kai akwatunan aure dankare da kaya na lefen gimbiya Zarah Bayero.
Kamar yadda aka tattaro, biyu daga cikin akwatunan na dankare da zinari da lu'u-lu'u da kuma tsabar kudi.
KU KARANTA: Duk yunkurin bata sunan Abba Kyari da mutuncinsa ba zai yi aiki ba, Fani Kayode
Malami ne ya shawarci jam'iyyar APC ta yi zabukanta na gundumomi
Dan kwamitin rikon kwaryar jam'iyyar APC, Mamman Tahir yace Antoni janar na kasarnan, Abubakar Malami ya shawarci 'yan jam'iyyar dasu fara zabukan gunduma.
An mayar da zabukan gundumomi na jam'iyyar APC ya kasance ranar Asabar, amma kuma akwai lauje cikin nadi, daya daga ciki shine ko dai kwamitin rikon kwarya wacce gwamna Mai Mala Buni su shirya taron ko akasin hakan.
Sai dai a ranar Juma'a a Abuja Tahir yace za a yi zabukan a ranar 31 ga watan Yulin 2021 kamar yadda aka shirya, Daily Trust ta wallafa.
Asali: Legit.ng