Cin amana: Yadda Shakikin aminin ma'aikacin banki ya sheke shi, ya birne shi a Yobe

Cin amana: Yadda Shakikin aminin ma'aikacin banki ya sheke shi, ya birne shi a Yobe

  • Da ace Abubakar Hassan ya san abinda zai faru dashi da bai amince da zama a gidan da aka kara shi ba a Damaturu
  • Hassan bai kai watanni 6 ba a gidan kwastam ajali ya riskeshi sakamakon halakashi da amininshi yayi
  • Al’amarin mai ban tsoro ya faru ne a jihar Yobe a ranar 22 ga watan Yulin 2021 kamar yadda ‘yar uwar mamacin ta shaida

Damaturu, Yobe - Idan da Abubakar Hassan ya san al’amarin da zai faru dashi da bai amince da zama ba a gidan da aka bashi ya zauna a Red Bricks, wani bangare na Damaturu babban birnin jihar Yobe.

Hassan bai wuci watanni 6 ba a gidan kawai wani yazo ya kashe shi. Abokai, ‘yan uwa da masoyan mamacin har yanzu suna cikin mamakin faruwar lamarin a ranar 22 ga watan Yulin 22 na 2021.

KU KARANTA: An gina APC kan karairayi, bacin sunan jama'a, ba za ta wuce 2023, Lamido

Kara karanta wannan

Dadiyata: Iyaye da Iyali sun koka game da halin tashin hankalin da suka shiga a shekaru 2

KU KARANTA: Rick Ross: Mawakin gambara da ya mallaki motoci 100 na alfarma, bashi da lasisin tuki

Cin amana: Yadda Shakikin aminin ma'aikacin banki ya sheke shi, ya birne shi a Yobe
Cin amana: Yadda Shakikin aminin ma'aikacin banki ya sheke shi, ya birne shi a Yobe. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Hotunan Ango Yusuf Buhari da amarya Zahra Bayero yayin wasan Polon bikinsu

'Yar uwar mamacin ta bada labarin abinda ta sani

Maryam Salihu, ‘yar uwar mamacin ta tabbatar wa da Daily Trust cewa an dade ana jan kunnensa akan abota da Umar Shaibu, wanda aka fi sani da Abba, wanda aka fi zargi kuma ya yi alkawarin daina alaka dashi.

Kamar yadda Maryam tace, lokacin da aka baiwa dan ’uwanta wurin zaman nan, bai mayar da kayanshi can ba saboda gidan yana da komai.

An bashi gidan dake Red Bricks duk da kayan cikin gidan a shirye. Saida ya zubar da duk kayan tsohon gidansa da ya tashi,” a cewarta.

Ta kara da bayyana yadda marigayin dan ’uwanta ya bata kyautar tsofaffin kujerunsa ya tura Abba ya kai mata. Maryam tace ranar ta fara ganin makashin dan ’uwanta da idanunta.

Kara karanta wannan

Cikin mako guda: 'Yan bindiga sun kashe mutum 48, da kona sama da gidaje 300 a Kaduna

A cewarta, bai wuci bayan makonni 2 ba da kashe dan ’uwanta sai Abba ya lallaba ya saci kayansa.

“Makonni 3 da suka gabata kanina ya sanar dani cewa Abba ya je gidansa ya satar masa suturu da wasu abubuwa. Har yana tunanin da cikin suturu akwai wanda na dinka masa.

A cewarta har budurwar ta sanar da yadda Abba ya saci kayan Abubakar kwanakin baya. Cikin hawaye Maryam ta bayyana ganin dan ’uwanta na karshe da tayi.

Abba ya bayyana yadda shi da wasu mutane 3 suka taru suka kashe shi.

Lokacin da muka je gidan, mu 4, mun je da niyyar mu saci injin mai samar da wuta. Ni da Modu muka fara shiga gidan. Mun shirya da cewa wasu zasu tsaya a kofa idan muka kwankwasa kofa ya bude sai mu buge shi mu shiga muyi satar.
Daya daga cikinsu yana rike da karfe da bigeshi saida na tabbatar ya kai kasa ashe sun kashe shi sai suka gudu. Bayan naga jini ne nace su nemi wuri mu birne shi.

Kara karanta wannan

Shugaba Muhammadu Buhari ya koma Abuja bayan mako daya a Daura

Malami ne ya shawarci jam'iyyar APC da tayi zabukanta na gunduma, Tahir

Dan kwamitin rikon kwaryar jam'iyyar APC, Mamman Tahir yace Antoni janar na kasarnan, Abubakar Malami ya shawarci 'yan jam'iyyar dasu fara zabukan gunduma.

An mayar da zabukan gundumomi na jam'iyyar APC ya kasance ranar Asabar, amma kuma akwai lauje cikin nadi, daya daga ciki shine ko dai kwamitin rikon kwarya wacce gwamna Mai Mala Buni su shirya taron ko akasin hakan.

Sai dai a ranar Juma'a a Abuja Tahir yace za a yi zabukan a ranar 31 ga watan Yulin 2021 kamar yadda aka shirya, Daily Trust ta wallafa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng