Bayan farmakin Kareto, sojoji sun kai samame maboyar Boko Haram a Gubio, sun yi barna

Bayan farmakin Kareto, sojoji sun kai samame maboyar Boko Haram a Gubio, sun yi barna

  • Dakarun sojin Najeriya sun kai samame maboyar 'yan Boko Haram dake Gubio inda suka yi musu gagarumar barna
  • An gano cewa miyagun sun kai farmaki kan tawagar sojojin a ranar Asabar, amma dakarun sun musu ruwan wuta ranar Lahadi
  • Har a halin yanzu ba a san yawan miyagun da aka sheke ba, sai dai majiyar sirri ta tabbatar da cewa an sheke 'yan ta'adda masu yawa

Gubio, Borno - Bayan farmakin Kareto, sojojin Najeriya sun sake shiryawa tare da kai babban farmaki kan mayakan ta'addanci na Boko Haram dake Gubio, PRNigeria ta ruwaito.

Miyagun 'yan ta'addan Boko Haram sun ji ruwan wuta bayan dakarun sojin Najeriya sun bankado maboyarsu dake Gubio a jihar Borno a ranar Lahadi.

KU KARANTA: An gano makuden kudin da sabon kulob din Ahmed Musa zai dinga biyansa duk Shekara

Bayan farmakin Kareto, sojoji sun kai samame maboyar Boko Haram a Gubio, sun yi barna
Bayan farmakin Kareto, sojoji sun kai samame maboyar Boko Haram a Gubio, sun yi barna. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Miyagu nawa suka sheka barzahu?

Har a halin yanzu ba a san yawan miyagun 'yan ta'addan da aka halaka ba. Sai dai wata babbar majiyar sirri ta sanar da PRNigeria cewa an yi wa 'yan ta'addan mummunar barna.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Yan Ta'addan ISWAP Sun Mamayi Sojoji Sun Bude Musu Wuta a Borno

An gano cewa a ranar Asabar ne 'yan Boko Haram suka kaiwa wata tawagar sojoji samame kan babbar hanyar Gubio zuwa Damasak dake yankin Kareto a arewacin jihar Borno.

Duk da ba a san yawan rayukan da suka salwanta ba a bangaren dakarun sojin, amma kamar yadda majiyar tsaron ta sanar, ta ce cike da dabara sojojin suka tsara yadda zasu kai farmaki maboyar miyagun a ranar Lahadi.

Dakarun sojin cike da shirin fada, bayan farmakin da aka kai musu na Kareto suka je har maboyar miyagun dake Gubio suka sakar musu ruwan wuta da motocin yaki," yace.

KU KARANTA: Rick Ross: Mawakin gambara da ya mallaki motoci 100 na alfarma, bashi da lasisin tuki

'Yan bindiga sun kai farmaki babban asibiti a Zamfara

Wasu miyagu da ake zargin 'yan bindiga ne sun kutsa babban asibiti gwamnati dake Dansadau a karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara a ranar Juma'a.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Rundunar soji ta saki hotunan yan ta’adda, matansu da yara da suka mika wuya ga sojoji a Borno

Daily Trust ta tattaro cewa miyagun sun yi awon gaba da wata ma'aikaciyar jinya da kuma wata mai jinyar mara lafiya.

Mazauna yankin sun sanar da cewa bayan 'yan bindigan sun shiga asibitin, 'yan bindigan sun fara neman likita ko ma'aikatan jinya.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel