Babbar magana: Kasar Saudiyya ta sake sanya sabuwar dokar Korona mai tsaurin gaske

Babbar magana: Kasar Saudiyya ta sake sanya sabuwar dokar Korona mai tsaurin gaske

  • Kasar Saudiyya ta sanya sabuwar +dokar Korona saboda yawaitar kamuwa da cutar
  • Kasar ta ce, a yanzu an haramta wa kowa zuwa ko ina sai har ya yi allurar rigakafin Korona
  • Kasar Saudiyya na ci gaba da daukar matakan rage yaduwar Korona a kasar tun farkon bullowarta

Gwamnatin Saudiyya ta ce daga ranar Lahadi ta 1 ga watan Agusta babu wanda zai shiga kantinan zamani ko kuma wuraren sana'o'i ko motar haya ko ofisoshin gwamnati sai wanda aka yi wa allurar rigakafin korona, BBC ta ruwaito.

Ma'aikatar cikin gida ta kasar ce ta bayyana hakan, tana cewa dole kowa ya fito a yi masa rigakafin ko a wanne yanki yake na masarautar.

Saboda fargabar sabuwar dokar, an karo yawan alluran rigakafin kuma ana samun dogayen layuka a Riyadh da sauran wurare.

Babbar magana: Kasar Saudiyya ta sake sanya sabuwar dokar Korona mai tsaurin gaske
Sarkin Saudiyya | Hoto: bbc.com/hausa
Asali: Twitter

Adadin wadanda aka yi wa allurar rigakafin cikakkiya a Saudiyya ba shi da yawa idan aka kwatanta da makonta na yankin Golf.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Annobar Korona ta barke a sansanin NYSC na jihar Gombe

Tun daga farkon bullar annobar, masarautar na daukar tsauraran matakan da suka kamata don dakile cutar ta Korona.

Ko a makon jiya, sai da aka yi wa mutane gargadi kan cewa za su iya fuskantar haramcin tafiya idan suka shiga Saudiyya daga kasashen da Saudiyyar ta hana zuwa.

Da duminsa: Annobar Korona ta barke a sansanin NYSC na jihar Gombe

A Najeriya kuwa, akalla membobin bautar kasa 25, ciki har da mai shayarwa, suka kamu da cutar Korona a sansanin NYSC na jihar Gombe da ke Amada, Karamar Hukumar Akko.

Da yake tabbatar da lamarin a ranar Asabar a wata tattaunawa ta musamman, Kwamishinan Lafiya, Dakta Habu Dahiru, ya ce an yi wa masu yi mutane 25 gwaji a cikin kwanaki ukun da suka gabata, Punch ta ruwaito.

Ya kara da cewa an tura su zuwa cibiyar killacewa mallakar jihar a cibiyar cututtuka na Idris Mohammed da ke Kwadon.

Kara karanta wannan

Tarihin kudaden Najeriya, tun zamanin da ake amfani da gishiri a matsayin kudi zuwa yanzu

Kwararrun likitocin Najeriya za su tsunduma yajin aiki

A wani labarin, Kungiyar Kwarrarun Likitoci ta MDCAN a Najeriya ta yi barazanar shiga yajin aiki na sai baba ya gani kan wata bukata da ta ke dashi na gyara tsarin albashin mambobinta, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban MDCAN na kasa, Farfesa Keneth Ozoilo, ya ba da wa’adin kwanaki 21 na shiga yajin aiki a taron manema labarai a Jos, babban birnin jihar Filato, ranar Litinin, 26 ga watan Yuli.

Ya ce an yanke shawarar bayar da wa'adin ne yayin taron gaggawa na kungiyar ta kasa da aka gudanar a ranar 19 ga Yulin 2021.

Asali: Legit.ng

Online view pixel