Amurka ba ta da ikon kame Kyari, hukumar kula da ayyukan 'yan sanda ta yi martani
- Hukumar kula da ayyukan 'yan sanda ta ce bata san komai game da zargin Amurka kan Abba Kyari ba
- Hukumar ta ce, har yanzu babu wanda ya mata bayani game da halin da ake ciki na zargin Abba Kyari
- Ta bayyana cewa, ya kamata a bi matakai ta hannunta matukar ana son lamarin ya tafi yadda ake so
Abuja - Biyo bayan takaddamar da aka samu daga rahoton Amurka da ke tuhumar Abba Kyari, Mataimakin Kwamishinan 'Yan sanda (DSP), Hukumar Kula da Ayyukan 'Yan sanda (PSC) a ranar Asabar, 31 ga Yuli ta yi martani kan takaddamar.
Vanguard ta ruwaito cewa hukumar ba ta sami rahoto na doka ba kuma mai ma'ana kan "bakon" zargin na Amurka mai umarnin kama Abba Kyari.
Legit.ng ta tattaro cewa PSC ta yi kira ga ofishin babban lauyan gwamnatin tarayya da ya jagorance ta kan batun tunda ita (hukumar) ita ce hukumar da ke da ikon ladabtar da jami'an 'yan sanda da suka yi kuskure.
Wani da ake zargi da zamba ta intanet, Ramon Olorunwa Abbas, wanda ake kira Hushpuppi, an ruwaito cewa ya shaida wa Hukumar Binciken Tarayyar Amurka (FBI) game da alakarsa da Kyari kan cafke wani da ake zargi da aikata zamba, Kelly Chibuzo Vincent.
Rahoton ya bayyana cewa PSC tana shirin gudanar da bincike na daban kan umarnin kotun Amurka ga FBI da ta kame Kyari kan zargin karbar cin hancin dala miliyan 1.1 da Hushpuppi ya bashi.
Jaridar The Nation ta kuma ruwaito cewa PSC ce ke da alhakin gudanar da aikin ladabtarwa da tsara manufofi da jagororin nadin mukamai a rundunar 'yan sandan Najeriya.
Amurka ta so a mika mata Abba Kyari ta bincike shi
Ko da yake Sufeto Janar na 'yan sanda, Usman Baba, ya ce hedkwatar rundunar ta fara bincike kan zargin, PSC ta ce har yanzu ba a yi mata cikakken bayani kan lamarin ba.
Kwamishinan kafafen yada labarai a hukumar PSC, Austin Braimoh ya ce hukumar ba za ta tsaya ga binciken IG na zargin da ake yi wa Kyari ba.
Ya ce dole ne a kawo rahoton da ya dace daga matakin da ya dace zuwa hukumar domin ta dauki mataki.
Braimoh ya ce:
"PSC ba ta da masaniya kan zargin da ake yi wa DCP Abba Kyari a yanzu. Saboda babu wani rahoto da ya dace da ke gaban Hukumar akan jami'in.
“Abin da muke ji kawai zargi ne daga kafafen yada labarai. Babu wata hukuma ta tsarin mulki da ke aiki da irin wannan zargin.
"Dole ne a kawo rahoto na gaskiya ga hukumar daga wani wuri ko wani. Baya ga haka, mun kawai ji cewa wata Kotun Amurka ta tuhume shi ko kuma ta ba da umarnin kama shi.
“Abin mamaki ne a gare ni cewa wata kotun Amurka za ta iya ba da umarnin a kama wanda ba dan kasar ta ba, dan Najeriya mazaunin Najeriya."
IGP ya nemi a gaggauta dakatar da Abba Kyari daga aiki
A wani labarin, sufeton 'Yan Sandan IGP Usman Alkali Baba, ya nemi a 'gaggauta' dakatar da Abba Kyari daga aiki bisa zargin karbar cin hanci da 'yan sandan Amurka ke yi masa kwanakin nan da ke da alaka da dan damfarar nan Abbas Roman Hushpuppi.
Baba, a cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Frank Mba ya fitar, ya ba da shawarar dakatar da Kyari nan take inda aka fara bincike akansa, in ji rahoton Daily Trust.
IGP ya kafa wani kwamati na mutum hudu karkashin jagorancin DIG Joseph Egbunike domin bincikar zargin da ake yi wa Abba Kyari, mataimakin kwamishinan 'yan sanda kuma shugaban tawagar tattara bayanan sirri ta 'yan sanda wato IRT.
Asali: Legit.ng