Da Duminsa: IGP ya nemi a gaggauta dakatar da Abba Kyari daga aiki

Da Duminsa: IGP ya nemi a gaggauta dakatar da Abba Kyari daga aiki

  • Sufeton 'yan sanda IGP Usman Alkali ya ba da umarnin a gaggauta dakatar da Abba Kyari
  • Wannan na zuwa ne yayin da korafe-korafe suka yi yawa kan zargin Abba Kyari da karbar rashawa
  • A halin yanzu, an kafa wani kwamitin bincike kan Abba Kyari, wanda zai ba da rahoto nan kusa

Abuja - Sufeton 'Yan Sandan IGP Usman Alkali Baba, ya nemi a 'gaggauta' dakatar da Abba Kyari daga aiki bisa zargin karbar cin hanci da 'yan sandan Amurka ke yi masa kwanakin nan da ke da alaka da dan damfarar nan Abbas Roman Hushpuppi.

Baba, a cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Frank Mba ya fitar, ya ba da shawarar dakatar da Kyari nan take inda aka fara bincike akansa, in ji rahoton Daily Trust.

IGP ya kafa wani kwamati na mutum hudu karkashin jagorancin DIG Joseph Egbunike domin bincikar zargin da ake yi wa Abba Kyari, mataimakin kwamishinan 'yan sanda kuma shugaban tawagar tattara bayanan sirri ta 'yan sanda wato IRT.

Kara karanta wannan

Watan Oktoba za'a yankewa Abbas Hushpuppi hukunci a Amurka

Da duminsa: IGP ya nemi a gaggauta dakatar da Abba Kyari daga aiki
Abba Kyari da Hushpuppi | Hoto: legit.ng
Asali: UGC

Cibiyar bincike ta kasar Amurka (FIB) ta nemi hukumomin Najeriya su bincike Kyari bisa alakar cin hanci Hushpuppi da kuma taimaka masa ta wata hanya.

Meye alakar Hushpuppi da Abba Kyari?

Hushpuppi ya bayyana cewa ya bai wa Mista Kyari rashawar makudan kudade yayin da hukumar tsaron FBI ta Amurka ta kama shi bisa zargin aikata damfara da zamba a kan kamfanoni da daidaikun mutane a wasu kasashe.

Sai dai, rundunar ta ce har yanzu tana daukar Abba Kyari a matsayin maras laifi har sai bincike ya tabbatar da laifin nasa, in ji BBC Hausa.

Yadda Abba Kyari ya turawa Hushpuppi asusun bankin wani don tura masa kudi

A wani labarin daban, Sabbin bayanai sun bayyana kan zargin da aka yiwa hazikin jami'un dan sanda, DCP Abba Kyari, a gaban kotun kasar Amurka.

Legit ta ruwaito muku cewa kotun Amurka ta ce shahrarren dan damfara, Abbas Ramoni, wanda akafi sani da Hushpuppi ya ambaci Abba Kyari cikin wadanda suka sha romon kudin damfarar $1.1m.

Kara karanta wannan

Hukumar hisbah ta damke wani mai kyamis da ke lalata da mata a Kano

Kyari kuwa a martaninsa, ya karyata wannan zargi inda yace ko kadan bai bukaci kudi hannun Hushpuuppi ba kuma bai amsa kudi hannunsa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel