Watan Oktoba za'a yankewa Abbas Hushpuppi hukunci a Amurka
- Kotun Amurka ta bayyana ranar yankewa Hushpuppi hukunci
- Hushpuppi ya amsa dukkan laifukan da ake zarginsa da su
- Ana tunanin za'a jefashi kurkukun akalla shekaru 20
Ofishin Antoni Janar na kasar Amurka a yankin California ya ce a watan Oktoba, 2021 za a yankewa Ramon Abbas, wanda akafi sani da Hushpuppi hukunci.
Diraktan yada labarin kotun, Thom Mrozek, ya bayyana hakan ga jaridar Punch a akwatin sako email ranar Juma'a.
Hakazalika kotun ta tabbatar da cewa ta umurci hukumar binciken FBI ta damke DCP Abba Kyari na Najeriya, bisa rawar da ya taka wajen damfara $1m da Hushpuppi yayi.
Thom Mrozek yace:
"Wani Alkalin kotun majistaren Amurka ya bada umurnin damke mutanen da ake zargi, har da Kyari."
"Hushpuppi yanzu haka ana shirin yanke masa hukunci a karshen Oktoba."
Jami'in kotun amma bai bayyana ko za'a gurfanar da Abba Kyari a kotu lokacin ba.
Hushpuppi ya amsa laifinsa a kotu, zai tafi gidan yari
Ramon Abbas, ya amsa laifuffukansa ya yarda bai da gaskiya, a shari’ar da ake yi da shi a Kalifoniya, Amurka.
Punch ta ce Ramon Abbas wanda aka fi sani da Hushpuppi ya amince ya aikata laifuffukan da ake tuhumarsa da su nan satar kudi, damfara da dai sauransu.
Kamar yadda takardun kotu suka nuna, Ramon Abbas ya tabbatar wa kotu cewa lallai bai da gaskiya.
DCP Abba Kyari na cikin wadanda na baiwa kudin cin hanci, Hushpuppi
Shahrarren mai damfarar yanar gizo, Abbas Ramoni, wanda akafi sani da Huspuppi, ya bayyana cewa hazikin dan sanda, DCP Abba Kyari, na cikin wadanda ya baiwa kudin cin hanci.
Hakan na kunshe cikin wasu takardun kotun gwamnatin Amurka.
Asali: Legit.ng