Ta nemi a raba aurenta da mijinta saboda yana shan sigari a dakinta, shi kuma ya nemi ta yi masa sabon aure

Ta nemi a raba aurenta da mijinta saboda yana shan sigari a dakinta, shi kuma ya nemi ta yi masa sabon aure

  • Wata uwargida mai suna Amina Aminu, ta nemi kotun Musulunci ta raba aurensu na shekaru biyu da watanni biyar da mijinta
  • Amina wacce ta zargi maigidanta Muhammad da sha mata sigari a daki da nuna kiyayya ga 'yan uwanta ta dau alkawarin biyansa sadakin N50,000 na ya bayar da aurensu
  • Sai dai kuma lauyan wanda ake kara ya nemi a raba auren bisa sharadin cewa za ta sake yi masa sabon aure tare da daukar dawainiyar bikin gaba daya

Wata mata mai matsakaicin shekaru, Amina Aminu, a ranar Talata ta gurfanar da mijinta, Umar Muhammad a gaban Kotun Shari’ar Musulunci da ke zaune a Magajin Gari, Jihar Kaduna, tana neman a raba aurensu.

Amina wacce ke zaune a Kaduna ta nemi hakan ne bisa zargin cewa mijin nata yana shan sigari a dakinta kuma ba ya son ’yan uwanta, jaridar The Nation ta ruwaito.

Amina ta nemi a raba aurenta da mijinta saboda yana shan sigari, shi kuma ya nemi ta yi masa sabon aure
Amina ta nemi a raba aurenta da mijinta saboda yana shan sigari kuma baya son yan uwanta aure Hoto: Thisday
Asali: UGC

Ta ce:

Kara karanta wannan

Labari Da Ɗuminsa: Kotu Ta Tura Sunday Igboho Gidan Yari a Kwatano

"Na tunkari wannan kotu ne ina neman saki saboda mijina ya ki canza halayensa.
“Ba zan iya rayuwa tare da shi ba. Zan biya shi N50, 000 da ya biya a matsayin sadakina shekaru biyu da watanni biyar da suka gabata don fansar kaina daga auren.
"Na ba shi dama sau da yawa don ya canza amma ba zai taba yin hakan ba."

Wanda ake kara, Muhammad, dan kasuwa wanda kuma ke zaune a cikin garin na Kaduna, ta hannun lauyansa, Nazifi Shehu, ya bukaci kotu da ta amsa bukatar mai karar na saki.

Shehu, ya roki kotu da ta umarci wacce ta shigar da karar da aura ma wanda yake karewa sabuwar mata, The Eagle online ya ruwaito.

“Wanda nake karewa yana son matarsa. Allah ya albarkace su da yarinya ‘yar wata tara, mun yi iya kokarinmu don ganin ta dawo gidan mijinta amma duk kokarin da muke yi ya ci tura.

Kara karanta wannan

Ina bukatar miji, Budurwa mai son daidaituwar 'yancin mata da maza ta koka

"Ya kamata ta samo masa wata matar sannan ta dauki nauyin dukkan kudaden da za a kashe na aure", in ji lauyan.

Alkalin kotun, Murtala Nasir, bayan ya saurari bangarorin, ya dage sauraron karar zuwa ranar 12 ga watan Agusta don yanke hukunci.

Ya umarci mai shigar da karar da ta nemi shawarar waliyinta kafin ya raba auren wanda a cewarsa shi ne kadai zabin da ya rage ga kotun.

A wani labari na daban, Mansurah Isah, Tsohuwar matar fitaccen jarumi a masana'antar Kannywood, Sani Danja, ta yi kira ga masu sukarta da su dakata hakanan da kiranta da wasu sunaye sabida ta zama bazawara, kamar yadda premium times ta ruwaito.

Mansura, wanda ta fara shirin fina-finai a ƙarshen shekarar 1990, da tsohon mijinta sun gina auren soyayya kafin su rabu a watan Mayun da ya gabata, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

A ranar Laraba, jarumar ta yi martani ga masu sukarta a wani rubuta da a buga a shafinta na kafar sada zumunta Instagram.

Kara karanta wannan

Allah Ya Isa Ban Yafe Ba, Fitacciyar Jarumar Kannywood Ta Yi Martani Ga Masu Sukarta

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng