Matar da ta haifi yara 9 a lokaci guda ta magantu, ta ce suna sa ‘pampers’ 100 da shan madara lita 6 a kullun

Matar da ta haifi yara 9 a lokaci guda ta magantu, ta ce suna sa ‘pampers’ 100 da shan madara lita 6 a kullun

  • Wata mata ‘yar kasar Mali, Halima Cisse, wacce ta haifi yara tara a lokaci daya, ta ce aiki ne babba kula da su
  • Cisse ta ce yaran, wadanda har yanzu shida daga cikinsu ke cikin kwalba, suna amfani da pampers guda 100 a kullum
  • Kula da marasa lafiyan na da tsada, kuma kudin asibitin su a halin yanzu ya kai KSh miliyan 150 (N378,922,650.60)

Wata mata 'yar kasar Mali da ta haifi yara tara a lokaci guda a ranar 5 ga watan Mayu, 2021, a kasar Maroko, ta bayyana cewa yaran suna amfani da ‘pampers’guda 100 a rana guda.

Halima Cisse, wacce ta haifi yaran a cikin asibitin Casablanca, ta shaida wa Daily Mail cewa jariran na shan lita shida na madara a kowace rana.

Matar da ta haifi yara 9 a lokaci guda ta magantu, ta ce suna sa ‘pampers’100 da shan madara lita 6 a kullun
Halima Cisse tare da mijinta Kader Arby da daya dagga cikin yaran Hoto: Simon Ashton for MailOnline.
Asali: UGC

A cewar matar mai shekaru 26, wacce a yanzu haka tana da ‘ya’ya goma, ta yi matukar kaduwa bayan ta haifi yaran guda tara, maza hudu da mata biyar.

Kara karanta wannan

Tauraruwar Kannywood Maryam Yahaya Ta Bayyana Cutar Dake Damunta Yasa Aka Ji Ta Shiru

Ta ce:

"Na yi matukar girgiza a lokacin da na gano cewa ina dauke da yara tara saboda na yi tsammanin guda bakwai ne."

Kula da yaran

Cisse ta bayyana cewa yayin da ta ga yadda ake haihuwar jariran ɗaya bayan ɗayan, tambayoyin da yawa sun shiga zuciyarta.

Ta kara da cewa:

"Ina sane da abin da ke faruwa kuma kamar dai jarirai ba masu karewa bane ke fitowa daga jikina."

Cisse ta yarda cewa tana mamakin yadda za ta kula da yaran yayin da take cikin ɗakin haihuwa.

Cisse ta ce "'Yar uwata na rike da hannuna amma abin da kawai nake tunani a kai shi ne ta yaya zan kula da su da kuma wadanda za su taimake ni."

Kusan watanni uku bayan haihuwar mai banmamaki, har yanzu shida daga cikin jariran suna cikin kwalba.

Cisse ta fada wa Daily Mail cewa kula da su yana da nauyi yayin da take nuna godiya ga kungiyar likitoci da ma'aikatan jinya da ke taimaka mata a kowane lokaci.

Kara karanta wannan

Ina bukatar miji, Budurwa mai son daidaituwar 'yancin mata da maza ta koka

Da take bayani kan yadda take kula da a kullun, Cisse ta ce ana ciyar da su duk bayan awa biyu a kan madarar gwangwani tunda ta rasa ruwan nono wata daya bayan haihuwa.

Hakanan ana canza musu pampers dun bayan awa biyu, jimlar guda 100 a rana. Hakanan ana duba lafiyarsu duk bayan awa uku.

Matar da ta haifi yara 9 a lokaci guda ta magantu, ta ce suna sa ‘pampers’100 da shan madara lita 6 a kullun
Halima Cisse tare da mijinta da ma'aikatan jinya Hoto: Simon Ashton for MailOnline.
Asali: UGC

Fiye da Naira Miliyan 378 ne kudin asibiti

Kula da yaran guda tara yana da tsada sosai, sun sami kimanin KSh miliyan 150 (N378,922,650.60) na kudin asibiti.

Sai dai, sa'ar da Cisse da mijinta Kader Arby suka samu, shine gwamnatin Mali ta yi alƙawarin ɗaukar nauyin kudin.

Ana sa ran jariran za su zauna a asibiti na tsawon watanni biyu masu zuwa.

Mata ta haifi yan uku bayan shekaru 11 da aure da yin bari sau 6

asu ma'aurata 'yan Najeriya da aka ambata da suna Mista da Misis Ogeah suna murnar zuwan ‘yan ukunsu bayan shekaru 11 da aure da kuma bari da dama.

Kara karanta wannan

Cikin mako guda: 'Yan bindiga sun kashe mutum 48, da kona sama da gidaje 300 a Kaduna

Wata 'yar uwarsu, Evelyn Odume, wacce ta ba da wannan labarin mai ban mamaki a ranar Lahadi, 11 ga Afrilu, ta bayyana cewa Allah ya ba shaidan kunya, Yabaleft ta ruwaito.

Shafin Twitter @Naija_PR ma ya yada labarin mai dadi a dandalin sada zumunta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel