Mataimakin gwamnan jihar Zamfara ya koka kan barazanar majalisa na tsige shi
- Mataimakin gwamnan jihar Zamfara ya koka kan yadda majalisar dokokin jihar ke kokarin tsige shi
- Ya bayyana cewa, majalisar ta yi biris da umarnin kotu na dakatar da batun tsige shi saboda kin sauya sheka
- Ya yi kira ga jama'a da su nemi majalisar jihar kan ta bi umarnin kotu da kuma tabbatar da doka da oda
Jihar Zamfara - Mataimakin gwamnan jihar Zamfara, Barista Mahdi Aliyu Muhammad Gusau, ya ce majalisar dokokin jihar na ci gaba da shirin tsige shi a ranar Alhamis duk da cewa hakan ya saba wa doka da umarnin kotu, Daily Trust ta ruwaito.
Da yake yi wa manema labarai bayani a ofishinsa a ranar Alhamis 29 ga watan Yuli, mataimakin gwamnan ya ce matakin da Majalisar Dokokin jihar ta dauka ya nuna rashin biyayya ga umarnin kotu kuma zai zama daidai da nuna rashin bin doka.
A cewarsa:
“Kamar yadda kuka sani, jam’iyyata ta PDP, ta gabatar da kara a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, tana kalubalantar dambarwar Majalisar Dokokin Jihar Zamfara kamar yadda aka tsara a yanzu don fara batun tsigeni ko kuma duk wani batu da ake a kaina a matsayin wanda aka zaba a karkashin jam'iyyar PDP.
“Babbar Kotun Tarayya ta ba da umarnin da ke jagorantar kula da halin da ake ciki a ranar 19 ga Yulin 2021.
“An ba da umarnin ga Babban Alkalin Jihar Zamfara, Majalisar Dokokin Jihar Zamfara da Gwamnan Jihar Zamfara.
“Duk da yanayin da ake ciki a yanzu, kakakin majalisar dokokin jihar ta Zamfara da majalisar sun fara daukar matakai na wuce gona da iri a kan batun, da kin bin umarnin kotu da kuma bayar da sakamakon karar.
“Ya zama tilas in jawo hankalin jama’a zuwa ga wannan mummunan yanayi tare da fatan 'yan kasa masu kyakkyawar niyya za su yi kira ga Majalisar Dokokin Jihar Zamfara don ba da umarni tare da nuna musu bukatar bin umarnin kotu."
Majalisar a Zamfara ta nemi matamakin gwamna ya bayyana a gabanta cikin sa'o'i 48
Majalisar Dokokin Jihar Zamfara ta ba Mataimakin Gwamna, Barista Aliyu Mahdi Gusau, wa’adin sa'o'i 48 ya bayyana a gabanta kan zargin aikata ba daidai ba a hukumance, Channels Tv ta ruwaito.
Zai bayyana a gaban majalisar ne kan wani taron siyasa da aka gudanar a ranar 10 ga watan Yuli, yayin da 'yan bindiga suka kai hare-haren kan al'ummomin Maradun a daidai lokacin da ake taron.
Karin wa’adin ranar Talatan ya biyo bayan kudirin da Mataimakin Shugaban majalisar, Nasiru Bello Bungudu ya gabatar don bayyana dalilin da ya sa ya gudanar da taron siyasa a yayin da kashe-kashen da suka faru a jihar.
PDP ta caccaki tafiyar shugaba Buhari zuwa Landan, ta ce ya yaudari 'yan Najeriya
A wani labarin, jam'iyyar PDP ta soki tafiyar shugaba Buhari zuwa Landan domin duba lafiya da kuma halartar wani taron koli kan fannin ilimi duk dai a Landan din, jaridar Punch ta ruwaito.
PDP ta ce, tafiyar shugaban ba komai bane face son amfani da albarkatun kasa don halartar taro wanda zai iya halartar ta yanar gizo; kamar yadda wadanda suka shirya taron suka tsara.
PDP ta kuma yi Allah wadai da Fadar Shugaban Kasa kan kokarin boye ganawarsa ta sirri da likitocinsa a karkashin taron da zai halarta, tare da yin tir da rashin cika alkawuran shugaba Buhari na zaben 2015 cewa ba zai je kasar waje domin duba likita ba.
Asali: Legit.ng