Sauya Sheka: PDP bata da hankali da take wa Matawalle barazana, Fani-Kayode

Sauya Sheka: PDP bata da hankali da take wa Matawalle barazana, Fani-Kayode

  • Femi Fani-Kayode yayi wa jam'iyyar PDP wankin babban bargo tare da kiranta da mara hankali
  • Fani-Kayode yace tsabar rashin lissafi ce ta sa PDP ke barazanar maka Matawalle a kotu kan sauye sheka
  • Tsohon ministan yace kadan PDP ta fara gani don nan gaba kadan wasu ababen mamaki zasu cigaba da bayyana

Tsohon ministan sufurin jiragen sama kuma jigo a jam'iyyar PDP, Femi Fani-Kayode, ya zagi jam'iyyarsa kan barazanar da take na maka Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara a gaban kotu kan sauya shekarsa zuwa jam'iyyar APC.

Fani-Kayode a jerin wallafar da ya dinga a shafinsa na Twitter, ya soki barazanar da ake wa Matawalle inda ya shawarci jam'iyyarsa da ta dage wurin janyo hankali, Daily Nigerian ta ruwaito.

"Barazanar da PDP ke yi na kai Bello Matawalle kotu a kan komawa jam'iyyar APC ta rashin hankali ce."

KU KARANTA: PDP ta kira taron gaggawa bayan wani gwamna na kokarin komawa APC

Sauya Sheka: PDP bata da hankali da take wa Matawalle barazana, Fani-Kayode
Sauya Sheka: PDP bata da hankali da take wa Matawalle barazana, Fani-Kayode. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Hotunan gwamnoni, ministoci da jiga-jigan da suka je fadar Kano nemawa Yusuf Buhari aure

"Dukkan gwamnonin PDP da suka ji zabe karkashin APC amma daga bisani suka koma PDP hakan dole ya shafesu ko kuma ku daina korafi.

“A lokacin da suke gwamnonin APC kuma suka bar jam'iyyarsu suka koma PDP, an dinga kwarzantasu.

“Amma yanzu da yake wasu gwamnonin PDP za su koma APC, ana musu barazana da shari'a. Wannan rashin adalci ne."

"A watanni uku da suka gabata, PDP ta rasa gwamnoni uku tare da wasu sanatoci da 'yan majalisa. Zan iya tabbatar muku da cewa abubuwan mamaki na nan zuwa nan gaba.

"Kamata yayi jam'iyyar ta zage wurin neman jama'a ba wai zagi da barazanar shari'a ba."

“Kamata yayi ku nemi wadanda suka fusata kuma bai dace ku zagesu ba ko kuma ku ce su yi abinda suka ga zasu iya ba. Wannan darasi ne gareku."

Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, jam'iyyar PDP na barazanar maka Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara gaban kuliya saboda sauya shekar da zai yi.

A wani labari na daban, gwamnatin jihar Kaduna ta musanta rahoto dake yawo na cewa ta tura jami'an tsaro domin musgunawa dalibai masu zanga-zanga a kwalejin ilimi, wanda hakan ya janyo ajalin dalibi daya.

Daily Trust ta ruwaito cewa, wannan yana zuwa ne bayan sa'o'i kadan da jami'an tsaro suka harbe wani dalibi daga cikin daruruwan dake zanga-zanga kan karin kudin makaranta.

A wani bayani ga manema labarai da kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan yayi, ya ce gwamnatin jihar Kaduna tana jiran bayanai domin su bata damar gano abinda ke kunshe a cikin rikicin da ya barke a Gidan Waya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel