Yadda Aka Kusa Kashe Tsohon Hadimin Gwamna Da Ya Ƙi Komawa APC Tare Da Gwamna

Yadda Aka Kusa Kashe Tsohon Hadimin Gwamna Da Ya Ƙi Komawa APC Tare Da Gwamna

  • Cif Mark Obi, tsohon hadimin Gwamna Ben Ayade ya tsallake rijiya da baya bayan an kai masa hari a gidansa
  • Yayansa, Emmanuel Obi, ya tabbatar cewa mashawarcin gwamna kan tsaron daji Thomas Obi Tawo, ne ya jagoranci yan daba suka kaiwa kaninsa hari
  • Emmanuel ya ce Tawo da yan daban sun kutsa gidan kaninsa sun masa duka sannan suka sare shi suka bar shi a kwance suna tunanin ya mutu

An kai wa tsohon mashawarci na musamman ga Gwamna Ben Ayade na jihar Cross Rivers, Cif Marki Obi, hari a garinsu da ke karamar hukumar Boki na jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Yayan Marki, Emmanuel Obi, ya tabbatar da afkuwar lamarin, yana mai cewa abin ya faru ne misalin karfe 10 na daren ranar Laraba.

Marki Obi, jigo a jam'iyyar PDP a jihar Cross River, ya ki komawa jam'iyyar All Progressives Congress (APC) tare da gwamnan.

Kara karanta wannan

Sauya Sheƙa: Wasu Ƴan APC Sun Cinnawa Tsintsiyarsu Wuta, Sun Ce Suna Neman Mafaka a Ƙarƙashin Lemar PDP

Yadda Aka Kusa Kashe Tsohon Hadimin Gwamna Ya Da Ƙi Komawa APC Tare Da Gwamna
Taswirar Jihar Cross Rivers. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Obi, ya kuma yi aiki a matsayin dan majalisar jihar sau biyu, sannan ya yi aiki a gwamnatin tsohon Gwamna Liyel Imoke.

A baya-bayan nan, Obi ya yi murabus a matsayin mashawarci na musamman ga Ayade.

Dan uwan wanda abin ya faru da shi ya ce:

"Thomas Obi Tawo, mashawarcin Gwamna Ayade kan tsaron daji ya kai wa dan uwa na mai shekaru 62 hari a gidansa misalin karfe 10 na dare.
"Ya taho tare da yan daba, dauke da adduna, suka kutsa gidan dan uwana suka lalata kayayyaki.
"Dan uwa na shi kadai ne a gida, ya kawo ziyara ne daga Calabar inda ya ke aiki a matsayin lauya.
"Bayan sun masa dukkan tsiya, sun kuma sare shi a jikinsa, kansa da hannu. Sun tafi sun bar shi suna tunanin ya mutu."

Daga bisani, yan kauyen suka kai Obi asibiti inda likita ya taimaka ya farfado da shi, amma ya bada shawarar a kai shi babban asibiti kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Sunday Igboho ya ji mumunan rauni lokacin DSS suka kai hari gidansa, Lauyansa

Babu tabbas idan harin na da alaka da siyasa amma Bessong Paul, wani jagora a garin, ya ce akwai yiwuwar rikicin da ke tsakaninsu na siyasa ne.

Boki ya yi kaurin suna wurin amfani da yan daba yana kaiwa mutane hari.

Babban mai sarautar gargajiya a karamar hukumar Boki, Mai martaba Atta Otu Fredaline ya ce ba a riga an masa bayani kan lamarin ba.

Dangi da 'yan uwa na saka 'yan siyasa satar kuɗin gwamnati, Ministan Buhari

A wani labarin daban, karamin ministan Kwadago da Samar da Ayyuka, Festus Keyamo SAN, ya ce matsin lamba da yan uwa da abokai ke yi wa mutane da ke rike da mulki ne neman su basu kudi ne ka karfafa musu gwiwa suna sata da aikata rashawa.

A cewar The Sun, Keyamo ya yi wannan furucin ne yayin jawabin da ya yi a ranar Laraba a Abuja yayin kaddamar da shirin 'Corruption Tori Season 2' da Signature TV da gidauniyar MacArthur suke daukan nauyi.

Kara karanta wannan

An damke kasurgumin dan bindiga da aka dade ana nema a jihar Sokoto

An kirkiri shirin ne domin wayar da kan mutane game da rawar da za su iya takawa wurin yaki da rashawa da cin hanci a Nigeria ta hanyar amfani da harsunan mutanen Nigeria.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel