Hawaye sun kwaranya yayin da Oba na jihar Lagas ya mutu sakamakon rashin lafiya da ba a bayyana ba a asibiti

Hawaye sun kwaranya yayin da Oba na jihar Lagas ya mutu sakamakon rashin lafiya da ba a bayyana ba a asibiti

  • Allah ya yi wa Oba na Iguruland, Aguda, yankin Surulere na jihar Legas, Alhaji Buhari Oloto rasuwa
  • Basaraken ya rasu ne a wani asibitin Lagas bayan ya yi fama da rashin lafiya da ba a bayyana ba
  • Mataimakin shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai wakiltar Lagos ta tsakiya, Hakeem Bamgbola ne ya tabbatar da mutuwar basaraken

Oba na Iguruland, Aguda, yankin Surulere na jihar Legas, Alhaji Buhari Oloto, ya mutu.

A cewar jaridar The Nation, an ruwaito cewa basaraken ya mutu ne a asibitin koyarwa na jami’ar jihar Legas (LASUTH), Ikeja.

Hawaye sun kwaranya yayin da Oba na jihar Lagas ya mutu sakamakon rashin lafiya da ba a bayyana ba a asibiti
Sarkin ya mutu ne a wani asibitin Ikeja
Asali: Facebook

Ya amsa kiran mahaliccinsa yana da shekaru 80 a duniya.

Mataimakin shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) (mai wakiltar Lagos ta tsakiya) Hakeem Bamgbola ne ya tabbatar da mutuwar basaraken.

Oba Oloto, wanda aka fi sani da Buhari Oloto kuma daga baya ake kiransa Abu Oloto, ya kasance sanannen mutum a cikin yanayin zamantakewar Legas fiye da shekaru 40.

Kara karanta wannan

Matasan NYSC 5 sun rasa rayukan sakamakon mumunan hadari a Abuja

Wani mamba a jam’iyyar APC a jihar Osun, Diran Olu Abiola, a cikin wani sakon da ya wallafa a shafin Facebook a ranar Alhamis, 29 ga watan Yuli, ya yi addu’ar Allah ya yiwa marigayi sarkin gafara.

Ya ce:

“Allah ya sa ka huta Alhaji buhari oloto,omo abulesheowo."

'Yan Najeriya da dama sun yi martani ga wallafar nasa.

Adeyemi Omoyele ya ce:

`` Ya mai girma oloto RIP. ''

Abiodun Okewole ya ce:

“Allahu Akbar, Allah ya sa ka huta baba.”

Aisha Oluwakemi Martin Olaniyan ta ce:

`` Allah ya sada sarki da Aljanat firdaous. ''

Wata jigon APC ta rigamu gidan gaskiya yayin jinya a kasar Amurka

A wani labari na daban, mun ji cewa jigo kuma ma'ajin jam'iyyar APC reshen jihar Legas, Misis Sumbo Ajose ta rigamu gidan gaskiya, Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Miyagu sun sheke dan takarar shugaban karamar hukuma na APC a Kaduna

Hakan ya faru ne kwanaki hudu da suka gabata lokacin da Najeriya ta rasa wani fitaccen danta, shahararren mawakin hip-hop, Olarenwaju Fasasi, wanda aka fi sani da"Sound Sultan," wanda shi ma ya mutu a Amurka bayan ya yi watanni yana fama da cutar kansa.

Ajose, 'yar siyasar da aka ce shekarunta sun haura 50, kamar yadda rahotanni suka nuna, ta mutu ne a kasar Amurka, a daren Talata, 13 ga watan Yuli, 2021.

Asali: Legit.ng

Online view pixel