Matasan NYSC 5 sun rasa rayukansu sakamakon mumunan hadari a Abuja

Matasan NYSC 5 sun rasa rayukansu sakamakon mumunan hadari a Abuja

Mumunan hadarin mota yayi sanadiyar mutuwar matasa masu shirin bautan kasa biyar a titin Abaji-Kwali dake Abuja yayinda suka nufi zuwa sansanin NYSC.

Diraktar yada labarai na NYSC, Adenike Adeyemi, ta bayyana hakan a jawabin da ta saki ranar Laraba, rahoton Punch.

Tace:

"Cikin jimami da bakin ciki Dirakta Janar, da daukacin hukumar NYSC ke jajantawa iyalan matasan dake shirin fara bautan kasa da suka rasa rayukansu a hadarin motan da ya auku misalan karfe 2 na daren yau, Laraba, 28 ga Yuli, 2020, a babban titin Abaji/Kwali."
"Hakazalika Dirakta Janar da daukacin hukumar na jajantawa gwamnatin Akwa Ibom da Imo kan wannan hadari."

Karin bayani na nan tafe....

Matasan NYSC 5 sun rasa rayukan sakamakon mumunan hadari a Abuja
Matasan NYSC 5 sun rasa rayukan sakamakon mumunan hadari a Abuja
Asali: Original

Asali: Legit.ng

Online view pixel