Da dumi-dumi: Wata jigon APC ta rigamu gidan gaskiya yayin jinya a kasar Amurka

Da dumi-dumi: Wata jigon APC ta rigamu gidan gaskiya yayin jinya a kasar Amurka

Jigo, kuma ma'ajin jam'iyyar APC reshen jihar Legas, Misis Sumbo Ajose ta rigamu gidan gaskiya. Vanguard ta ruwaito.

Hakan ya faru ne kwanaki hudu da suka gabata lokacin da Najeriya ta rasa wani fitaccen danta, shahararren mawakin hip-hop, Olarenwaju Fasasi, wanda aka fi sani da"Sound Sultan," wanda shi ma ya mutu a Amurka bayan ya yi watanni yana fama da cutar kansa.

Da dumi-dumi: Wata jigon APC ta rigamu gidan gaskiya a kasar Amurka
Jam'iyyar APC | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Ajose, 'yar siyasar da aka ce shekarunta sun haura 50, kamar yadda rahotanni suka nuna, ta mutu ne a kasar Amurka, a daren Talata, 13 ga watan Yuli, 2021.

A cewar rahotanni, ta kasance tana jinyar wani rashin lafiya da ba a bayyana ba na tsawon wani lokaci kuma tana gadon asibitin tana karbar magani a lokacin da ta mutu.

Sakataren yada labarai na jam'iyyar, Mista Seye Oladejo, ya tabbatar da mutuwar ya kuma bayyana jimami da bakin cikin mutuwarta

Cikakkun bayanai na nan tafe...

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel