Jim kadan baya sake Zakzaky da matarsa, sun cilla wani boyayyen wuri a Abuja

Jim kadan baya sake Zakzaky da matarsa, sun cilla wani boyayyen wuri a Abuja

  • Bayan da kotu ta wanke El-Zakzaky da matarsa a jiya, tuni sun cilla babban birnin tarayya Abuja
  • Rahotanni sun ce, malamin ya tafi tare da matarsa zuwa wani wurin da ba a bayyana ba a Abuja
  • A karo na farko, El-Zakzaky da matarsa sun samu 'yanci bayan tsarewa ta shekara biyar a gidan gyaran hali

Shugaban kungiyar Musulunci ta Islamic Movement in Nigeria (IMN) Ibrahim El-Zakzaky da matarsa, Zeenat, sun bar jihar Kaduna zuwa wani wurin da ba a bayyana ba a cikin babban birnin tarayya, Abuja.

Wannan na zuwa ne bayan El-Zakzaky da matarsa Zeenat sun sake samun ‘yanci a ranar Laraba 28 ga watan Yuli daga Cibiyar Gyaran Hali da ke Kaduna biyo bayan sallamar da babbar kotun jihar Kaduna ta yi musu.

Lauyan su, Femi Falana (SAN), a ranar Laraba ya fadawa SaharaReporters cewa malamin da matarsa sun bar Kaduna zuwa wani wurin da ba a bayyana ba bayan sun kwashe shekaru biyar a tsare ba bisa ka'ida ba.

Kara karanta wannan

El-Zakzaky: Lauyoyin Shehin Shi'a za su nemi diyya daga wajen Gwamnatin El-Rufai a Kotu

Jim kadan baya sake Zakzaky da matarsa, sun cilla wani boyayyen wuri a Abuja
Zakzaky da Matarsa | Hoto: qed.ng
Asali: UGC

Wata majiya a ranar Alhamis ta shaida cewa El-Zakzaky da matarsa, Zeenat, sun koma wani wurin da ba a bayyana ba a Abuja.

A cewar majiyar:

“El-Zakzaky da matarsa sun bar Kaduna sun koma wani wurin da ba a bayyana ba a Abuja bayan kotu ta wanke su kuma ta sallame su."

Yadda Kotu ta wanke Sheikh Zakzaky da matarsa, ta umarci a sake su

Rahotanni da muke samu sun bayyana cewa, a yau 28 ga watan Yuli, an yanke hukunci kan Zakzaky da matarsa, inda tuni aka wanke su daga zargi, in ji gidan talabijin Channels.

A cewar lauyan Zakzaky, Barista Sadau Garba, kotun ta wanke waɗanda ake zargin daga zargi takwas da gwamnatin Jihar Kaduna ta gabatar mata.

Rahoton ya ce tuni bayan yanke hukuncin aka zarce da Zakzaky zuwa gida nan take, kuma ba a tsaya sauraran 'yan jarida ba.

Kara karanta wannan

Yadda 'yan Najeriya za su iya amfani da zaben 2023 don gyara kuskuren da suka yi, Bishop Kukah

Tun farko, ba a 'yan jarida da sauran jama'a damar shiga zauren kotun ba. A cewar rahotanni, mai shari'a Gideon Kurada ne ya jagoranci shair'ar cikin sirri.

Yadda zaman kotu ke tafiya yayin shari'ar Abduljabbar a Kano

A wani labarin, Gwamnatin jihar Kano ta gurfanar da Malami, Sheikh AbdulJabbar Nasir Kabara gaban kotun Shari'ar Musulunci a ranar Laraba, 28 ga watan Yuli, 2021.

Wannan ya biyo bayan damkeshi da hukumar yan sanda tayi gabanin bikin Sallar Layya a ranar 17 ga Yuli, 2021.

A halin yanzu, ana ci gaba da sauraran abubuwan dake faruwa daga kotun. Kamar yadda BBC ta ruwaito, Alkali Sarki Yola ya bayar da umarnin a shiga da Sheikh Albduljabbar cikin akwatin wanda ake kara ke tsayawa.

Kuma, Aisha Mahmud ita ce ke jagorantar lauyoyin gwamnatin Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel