El-Zakzaky: Lauyoyin Shehin Shi'a za su nemi diyya daga wajen Gwamnatin El-Rufai a Kotu

El-Zakzaky: Lauyoyin Shehin Shi'a za su nemi diyya daga wajen Gwamnatin El-Rufai a Kotu

  • Lauyoyin Sheikh Ibrahim El-Zakzaky suna shirin sake shiga kotu da Gwamnati
  • Wannan karon za a bukaci diyya a dalilin tsare Malamin da aka yi na shekaru 6
  • Wasu daga cikin masu kare shugaban kungiyar IMN su na ganin an zalunce shi

Kaduna - Daya daga cikin lauyoyin da suka tsaya wa Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da Zeenat El-Zakzaky ya ce za su shigar da karar gwamnatin Kaduna.

Lauyoyi za su bidi hakkin Zakzaky da uwargidarsa

Marshal Abubakar wanda ya wakilci babban lauyan malamin da mai dakinsa, Femi Falana, SAN, ya yi magana da Vanguard bayan an kammala shari’ar.

Barista Marshal Abubakar ya yi wannan bayani ne ganin Alkalin kotu ta wanke Ibrahim El-Zakzaky da iyalinsa daga zargin da gwamnati ke yi masu.

Bayan haka wata daga cikin masu kare malamin, Sadau Garba, ta ce Ibrahim El-Zakzaky zai koma kotu, ya nemi gwamnatin Kaduna ta biya sa diyya.

Kara karanta wannan

Cikakken Bayani: Yadda Kotu ta wanke Sheikh Zakzaky da matarsa, ta umarci a sake su

Garba ta ce Shehin malamin da mai dakinsa, Zeenat Ibrahim El-Zakzaky za su nemi hakkin cin zarafi da muzguna masu da aka yi a yayin da suke tsare.

Da take magana a Abuja, Lauyar ta ce a cikin shaidun da su ka gabatar da hujjoji a kotu, babu wanda ya tabbatar da zargin da ke wuyan Sheikh Zakzaky.

“Duk cikin shaidun da aka gabatar, babu wanda ya tabbatar da cewa sun aikata laifin, don haka kotu ta wanke, kuma ta saki Sheikh Zakzaky da matarsa.”

Ibrahim El-Zakzaky
Shehin kungiyar IMN, Shi'a, Ibrahim El-Zakzaky

“Amma duk da haka za mu nemi hakki a hannun gwamnatin Kaduna na zalunta da muzugunawar da suka yi wa wanda muke kare wa (Ibrahim Zakzaky).”
“Yanzu suna bukatar su tafi gida, su ‘dan samu hutu, sannan su tafi asibiti domin a duba lafiyarsu.”

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa da aka nemi jin ta bakin babban lauyan da ya tsaya wa gwamnati a shari’ar, Dari Bayero, amma bai iya cewa uffan ba.

Kara karanta wannan

An tsaurara tsaro yayinda ake zaman yanke hukunci kan Sheikh Ibrahim ElZakzaky da Matarsa yau

Shari'ar Zakzaky da Gwamnatin Kaduna ta zo karshe

A jiye Laraba, 28 ga watan Yuli, 2021, rahotanni su ka tabbatar da cewa, kotu ta wanke malamin mazhabar shi'an, Ibrahim Zakzaky, daga zargin da ake yi masa.

Haka zalika kotu ta wanke matar malamin da yake tsare tun 2015, ta bada umarni a sake su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel