Kai tsaye: Yadda zaman kotu ke tafiya yayin shari'ar Abduljabbar a Kano

Kai tsaye: Yadda zaman kotu ke tafiya yayin shari'ar Abduljabbar a Kano

Gwamnatin jihar Kano ta gurfanar da Malami, Sheikh AbdulJabbar Nasir Kabara gaban kotun Shari'ar Musulunci a ranar Laraba, 28 ga watan Yuli, 2021.

Wannan ya biyo bayan damkeshi da hukumar yan sanda tayi gabanin bikin Sallar Layya a ranar 17 ga Yuli, 2021.

Kai tsaye: Yadda zaman kotu ke tafiya yayin shari'ar Abduljabbar a Kano
Sheikh Abduljabbar | Hoto: bbc.com/hausa
Asali: UGC

A halin yanzu, ana ci gaba da sauraran abubuwan dake faruwa daga kotun.

Kamar yadda BBC ta ruwaito, Alkali Sarki Yola ya bayar da umarnin a shiga da Sheikh Albduljabbar cikin akwatin wanda ake kara ke tsayawa.

Kuma, Aisha Mahmud ita ce ke jagorantar lauyoyin gwamnatin Kano.

A nasa bangare, Abduljabbar, lauyoyinsa guda tara, wadanda suka hada da:

  1. Sale Mohammad Bakaro
  2. Yahuza mohd Nura
  3. Bashir Sabi'u
  4. RS Abdullahi
  5. Y I Abubakar
  6. Zaubairu Abubakar
  7. Ya'u Abdullahi Umar
  8. B S Ahmad
  9. Umar Usman.

An dage shari'ar Abduljabbar zuwa wasu makwanni masu zuwa

Lauyar gwamnati ta bayyana dalilan da yasa ta roki a dage shariar zuwa wani lokaci in da take cewa:

"Mun saurari jawabansa, kuma bayanansa azarbabi ne. Mun nemi kotu ta dage shari'ar ne domin mu kawo tuhumar da muke yi masa.
"Ai caji ya kunshi dukkan wani bayani da muke bukata. Lauyan wanda ake kara ba shi ne zai fada mana yadda za mu tsara kararmu ba.
Kuma muna rokon kotu ta ba mu 25 ga watan Agusta, 2021, domin a ci gaba da shari'a.

Bayan doguwar caccaka tsinke, Alkali ya gamsu da bayanai daga dukkan bagarori, ya kuma yanke hukunci, inda ya amince da dage shari'ar zuwa wani lokaci.

BBC ta ruwaito cewa, Alkali ya dage shari'ar har zuwa nan da makwanni uku, wato za a sake zama ranar 18 ga watan Agustan wannan shekara.

Hakazalika, malamin zai ci gaba da zama a gidan gyaran hali. Dukkan bangarori sun gamsu.

An bai wa lauyoyin Abduljabbar damar yin magana a gaban kotu

Bayan sauraran bukatar da Lauyar gwamnatin jihar Kano, Aisha Mahmud, Alkali ya bai wa lauyoyin Abduljabbar magana.

Ya bayyana kokensa cewa, lauyar gwamnati na son kawo tsaiko a wannan shari'a, domin kuwa an tsare Abduljabbar amma ba a samu damar hada shaidu ba.

BBC ta kuma ruwaito shi yana cewa:

"An kawo wanda ake kara kwana 12 da suka gabata, amma abin bakin ciki ne masu gabatar da kara ba su shirya tuhumar da suke magana ba, wannan ya nuna cewar so suke su kawo tsaiko, ba so suke a yi shari'ar ba.
"Wanda ake kara yana tsare a gidan yari bisa umarnin kotu, wannan shi ne abin da muke jayayya a kai game da bayanin mai gabatar da kara."

Lauya Sale Bakaro ne ya bayyana haka, ya kuma bukaci a bi ka'idojin da aka tanada domin tabbatar da adalci a shari'ar, yana mai ishara suratul Hadid, Aya ta 20 ta Al-Kur'ani, ayar da ke an saukar da Al-Kur'ani ne domin a ayi adalci.

Lauyar gwamnati ta so ta yi tsokaci kan batu, amma Alkali ya dakatar da ita, ya ce sai ya dawo ta kanta, yana mai martanin cewa, zai yi wa kowa adalci.

Daga nan lauyan Abduljabbar ya nemi lauyar gwamnati ta gabatar dukkan shaidu, ciki har da na sauti ga kotu.

Alkali ya bukaci lauyoyin gwamnati su gabatar da shaidunsu

Bayan da aka Abduljabbar tuhumi Abduljabbar tun zaman farko, ya musanta zargin, yayin da a yau, Alkali ya bukaci lauyoyin gwamnati su bayyana shaidunsu ga kotu.

An BBC ta ruwaito, Lauya a bangaren gwamnati, Aisha Mahmud ta bayyana wata bukatar a masu lokaci domin samun damar gabatar da shaidu, inda take cewa:

"Mun samu dukkan bayanin shari'ar da ake kuma muna neman kotu ta ba mu wata rana domin gabatar mata da shaidu. Hakan zai ba mu dama mu hada bayananmu tare da tuhumar da muke yi wa Sheikh Abduljabbar."
Online view pixel