Rahoton Sirri: 'Yan bindiga daga Zamfara sun fara zuwa Borno karbar horo daga ISWAP

Rahoton Sirri: 'Yan bindiga daga Zamfara sun fara zuwa Borno karbar horo daga ISWAP

  • Rahotanni daga jami'an tsaro sun bayyana cewa, 'yan bindiga sun soma zuwa Borno domin karbar horo
  • A cewar wata sanarwa, an ce 'yan bindiga suna tattaki zuwa jihar Borno domin 'yan ISWAP su horar dasu ta'addanci
  • Wannan wasu bayanai na sirri daga hukumar shige da fice ta kasa (NIS) mai lamba NIS / HQ / CGI / 943

Jami’an tsaro sun samu nasarar gano wasu bayanan sirri game da yadda wasu ‘yan bindiga ke shigowa daga jihar Zamfara domin halartar shirin horas da 'yan ta’adda a jihar Borno.

A cewar wani rahoto na PRNigeria, wasu daga cikin ‘yan fashin sun riga sun bar jihar ta arewa maso yamma zuwa jihar ta arewa maso gabas domin samun horo a karkashin kulawar ISWAP-Boko Haram.

Rahoton ya nuna cewa Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS), ta samu ingantattun bayanan sirri.

Babbar magana: ISWAP za su soma horar da 'yan bindiga, in ji rahoton sirri
'Yan ta'addan ISWAP | Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

A cikin wata sanarwa mai mai lamba NIS / HQ / CGI / 943, rahoton ya ambato hukumar ta NIS tana kira ga kwanturololinta ta da su kara sanya ido a wuraren da suke karkashin ikonsu tare da tattara bayanan da za su taimaka wajen kiyaye rayuka da dukiyoyi.

Kara karanta wannan

Miyagu sun bi shahararren manomi har gonarsa sun sheke shi a Taraba

Takardar wacce aka yiwa lakabi da "Yunkurin 'Yan bindiga daga Zamfara zuwa Borno don horarwa daga Boko Haram" tana dauke dasa hannu ne daga wani jami'i ACG UA Auna.

Don haka bayanin ya umarci kwanturololin da su tabbatar sun gabatar da muhimman bayanai cikin hanzari don kula da Kwanturolan Janar na Hukumar Shige da Fice yayin da suka bayyana.

Rundunar sojin Najeriya ta karyata sakin 'yan Boko Haram, ta fayyace gaskiya

A ranar Alhamis din da ta gabata ne Sojojin Najeriya suka karyata rahotannin sakin mayakan Boko Haram da aka kama a Borno, Daily Nigerian ta ruwaito.

Wata sanarwa dauke da sa hannun Onyema Nwachukwu, Darakta, Jami’in Hulda da Jama’a na Soji, ta ce rahotannin karya ne kuma wani mummunan yunkuri ne na dakile tarbiyyar sojoji da kuma tozarta sojojin na Najeriya.

Ya ce rundunar Soji ba ta da niyyar shiga batutuwa tare da wadanda suka kitsa labaran na karya amma za su yi kokarin daidaita bayanan.

Kara karanta wannan

Matafiya tara aka sace a hanyar Sokoto-Gusau ba 60 ba – ‘Yan sanda

Domin magance matsalar tsaro, Najeriya za ta fara amfani da 'Robot' wajen yakar tsageru

A wani labarin, Majalisar Dattijan Najeriya ta ce Ma'aikatar Sadarwa ta kafa wata cibiya da za ta rika aiki da butumbutumi da basirar na'ura don yaki da matsalolin tsaro a kasar, sashen Hausa na BBC ya ruwaito.

Najeriya dai na ci gaba da fama da matsalolin tsaro da suka hada da garkuwa da mutane don kudin fansa da hare-haren 'yan bindiga musamman a arewacin kasar da ma ayyukan 'yan kungiyar Boko Haram/ISWAP a yankin arewa maso gabashin kasar.

Kawo yanzu, sama da dalibai 1,000 ne aka sace daga makarantu a arewacin Najeriya tun daga watan Disamban 2020.

Sanarwar ta ce:

“An sanar da Sojojin Najeriya (NA) game da wata kafar yada labarai da ke zargin cewa NA ta mika tsoffin mayakan Boko Haram 1009 ga gwamnatin jihar Borno.
“Rahoton ya kuma yi zargin cewa an yi taron sakin cikin sirri. Wannan rahoton a bayyane yake yana daya daga cikin irin kokarin da ake yi na dakushe kokarin sojoji da kuma tozarta NA, ta hanyar ba da rahotannin da ba su da tushe da kuma bayanan da ba su dace ba.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace sojojin Najeriya 2 akan wata babbar hanya a Borno

"Ba shakka cewa ayyukan da ake yi na magance kayar baya da ta'addanci (CTCOIN) a yankin Arewa maso Gabas ya kai ga kame wadanda ake zargi da ta'addanci / masu tayar da kayar baya."

Asali: Legit.ng

Online view pixel