'Yan bindiga sun sace sojojin Najeriya 2 akan wata babbar hanya a Borno

'Yan bindiga sun sace sojojin Najeriya 2 akan wata babbar hanya a Borno

  • 'Yan bindiga sun sace sojojin kasa 2 na Najeriya a kan babbar hanyar Maiduguri zuwa Damaturu
  • Kamar yadda aka gano, sun shiga motar farar hula ne a kan hanyarsu ta zuwa Kano yayin da lamarin ya faru
  • Sai dai tuni an damke direban motan saboda ganowa da aka yi yana da alaka da 'yan bindigan da suka tare su

Borno

Jami'an rundunar sojin kasa na Najeriya guda biyu, Bello Abubakar da Oyediran Adedotun sun shiga hannun 'yan bindiga a kan babbar hanyar Maiduguri zuwa Damaturu a yankin Goni Masari dake Borno.

Sojojin da aka yi garkuwa dasu suna kan hanyarsu ta zuwa Kano ne a wata motar farar hula wurin karfe 5 na yammacin ranar Asabar, kamar yadda sakon birged ta 29 ya nuna kuma SaharaReporters ta ruwaito.

KU KARANTA: Ruwan daloli: Bidiyon bahaushe yana watsi da daloli a liyafar biki ya janyo cece-kuce

Kara karanta wannan

Masu garkuwa da mutane a Abuja sun fara karbar kudin fansa ta banki

'Yan bindiga sun sace sojojin Najeriya 2 akan wata babbar hanya a Borno
'Yan bindiga sun sace sojojin Najeriya 2 akan wata babbar hanya a Borno. Hoto daga tribuneonlineng.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Masu garkuwa da mutane a Abuja sun fara karbar kudin fansa ta banki

Fasinjoji sun sanar da sojoji

An gano cewa fasinjojin dake cikin motar sun zargi direban yana da alaka da 'yan bindigan, lamarin da yasa fasinjojin suka sanar da sojojin dake sansanin Mainok.

Amma kuma dakaru na bataliya ta musamman ta 134 wadanda suka samu jagorancin kwamandansu sun gaggauta zuwa wurin amma tuni 'yan bindigan sun bar yankin.

An cafke direban mota

"An baiwa sojojin karamin hutu ne lokacin da lamarin ya faru. An gano cewa tuni aka bazama neman sojojin yayin da aka kama direban motar kuma ana bincikarsa," takardar da sojojin suka fitar ta bayyana.

Ba tare da bata lokaci ba dakarun dake yankin Mada/Matari suka kama direban tare da kwace abun hawansa.

Har yanzu sojojin basu san inda aka yi da sojoji biyun ba tare da sauran fasinjojin amma kuma an ga katin shaidar aiki na Abubakar a cikin motar, Tribune Online ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Hotunan 'Ɗan Sanda' Da Sojoji Suka Kama Da Harsashi 220 Da Gurneti a Borno

'Yan sanda sun gayyaci Muhuyi Rimingado

A wani labari na daban, rundunar 'yan sandan jihar Kano ta gayyaci tsohon shugaban hukumar karbar korafi da yaki da rashawa na jihar Kano, PCACC, Muhuyi Magaji Rimingado, domin ya amsa wasu tambayoyi kan zargin yin rahoton asibiti na bogi.

Majiyoyi daga rundunar 'yan sandan ta sanar da Daily Nigerian cewa a halin yanzu Rimingado yana ofishin 'yan sanda dake Bompai domin amsa wasu tambayoyi.

Yayin da Rimingado ya amsa kiran 'yan sandan, majalisar jihar a ranar Litinin ta aminta da sallamar shi duk da umarnin da kotu ta bada na hana cigaba da tuhumarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel