Miyagu sun bi shahararren manomi har gonarsa sun sheke shi a Taraba

Miyagu sun bi shahararren manomi har gonarsa sun sheke shi a Taraba

  • Wasu miyagu da ba a san ko su waye ba sun sheke fitaccen manomi kuma dan kasuwa a jihar Taraba
  • An gano cewa miyagun sun bibiyeshi har zuwa gona inda suka sheke shi ba tare da sun taba ko sisi daga kudin jikinsa ba
  • Mazauna yankin sun sanar da cewa sun ga wasu mutane uku a kan babur sun bar gonar yayin da suka ji ihun neman taimakonsa

Gasssol, Taraba - Wani shahararren manomi mai suna Saminu Barjanga dake kauyen Barjanga a karamar hukumar Gasssol dake jihar Taraba ya halaka bayan wasu sun je har gonarsa sun kashe shi.

Lamarin ya kara bada tsoro tare da firgita manoman dake yankin.

Daily Trust ta tattaro yadda manomin kuma fitaccen dan kasuwan ya mallaki shaguna a wurare daban-daban dake MutumBiyu, babban birnin Gassol.

KU KARANTA: Da duminsa: Karin daliban Kaduna 3 sun tsero daga hannun masu garkuwa da mutane

Kara karanta wannan

Da duminsa: Karin daliban Kaduna 3 sun tsero daga hannun masu garkuwa da mutane

Miyagu sun bi shahararren manomi har gonarsa sun sheke shi a Taraba
Miyagu sun bi shahararren manomi har gonarsa sun sheke shi a Taraba. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Gwamnonin PDP: Buhari ya mayar da fadar shugaban kasa sakateriyar APC

An taba sace shi a gonar a shekarar da ta gabata

A shekarar da ta gabata ne aka sace Barjanga a wannan gonar kuma an gano cewa sai da ya biya naira miliyan bakwai kafin a sake shi.

Majiyoyi daga iyalansa sun sanar da Daily Trust cewa marigayi Barjanga ya bar shagonsa da sassafe a ranar Litinin inda ya nufa gonar domin duba halin da take ciki amma sai aka kai masa farmaki.

Majiyoyi sun ce ta yuwu bibiyarsa makasan suka yi

Majoyiyin sun ce ta yuwu makasan sun bibiyi Barjanga tun daga MutumBiyu har zuwa gonarsa.

Majoyoyin sun ce wasu jama'a dake zama kusa da gonar marigayin sun ji ihun wani yana neman taimakon a cikin gonar.

Daily Trust ta tattaro cewa wasu mutum uku da ake zargi sun tsere a kan babur daga gonar inda aka kashe manomin.

Kara karanta wannan

Masu garkuwa da mutane a Abuja sun fara karbar kudin fansa ta banki

Barjanga tuni ya rasu yayin da masu cetonsa suka isa isa gonar kamar yadda majiyoyi suka ce. An samu makuden kudi a jikin manomin yayin da aka isa wurin da yake.

A wani labari na daban, Tunde Bakare, shugaban cocin Citadel Global Community, ya ce Ubangiji ya juyawa shugaban kasa Muhammadu Buhari baya.

A yayin jawabi a cocinsa wacce a da aka sani da Latter Rain Assembly, Bakare yace zai yi fito-na-fito da shugaban kasa kuma ya ga wanda zai bibiyesa kamar yadda aka saba yi wa duk wanda yayi magana a kasar nan.

Karfin iko ba a hannunka yake ba, kaine dai mai baiwa dakarun sojin kasa umarni, kuma baka isa ba idan ba a zabeka ba. Babban ofishi a kasar nan shine na dan kasa. 'Yan Najeriya zasu tashi kuma su bukaci hakkinsu.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel