EFCC ta daskarar da asusun bankin 'yar majalisa bayan ta siya motar N1bn

EFCC ta daskarar da asusun bankin 'yar majalisa bayan ta siya motar N1bn

  • Hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta daskarar da asusun 'yar majalisa bayan siyan motar N1bn
  • An gano cewa tuntuni hukumar EFCC ta gayyaci daraktar kudi ta majalisar jihar Oyo amma ta ki zuwa
  • Bincike ya nuna cewa kakakin majalisar ya hada kai da ita wurin siyan tsoffin motoci inda yace sabbi ne ga 'yan majalisar

Ibadan, Oyo - Daga cikin binciken siyan motocin da majalisar jihar Oyo tayi, hukumar yaki da rashawa da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC ta daskarar da asusun bankin daraktan kudi da asusu na majalisar jihar.

Tribune Online ta ruwaito cewa EFCC ta daskarar da asusun bankin daraktan kudi ta majalisar wacce ta ki amsa gayyatar da hukumar tayi mata.

Daskarar da asusun bankin na hana mutum cire kudi daga asusun bankinsa gaba daya.

KU KARANTA: Ubangiji ya juyawa Buhari baya, Fasto Bakare ya bayyana a sabon bidiyo

Kara karanta wannan

Matar tsohon minista ta kwanta dama tana da shekaru 91 a duniya

EFCC ta daskarar da asusun bankin dan majalisa bayan ya siya motar N1bn
EFCC ta daskarar da asusun bankin dan majalisa bayan ya siya motar N1bn. Hoto daga tribuneonlineng.com
Asali: UGC

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun sace sojojin Najeriya 2 akan wata babbar hanya a Borno

Ana zarginsu da siyo tsoffin motoci a matsayin sabbi

Daraktan tana daya daga cikin jami'an majalisar da ake tuhuma bayan an mika wani korafi na cewa kakakin majalisar ya hada kai da wasu jami'an gwamnati wurin samar da tsoffin motoci a matsayin sabbi ga 'yan majalisar.

Kamar yadda Tribune Online ta wallafa, wani jami'in hukumar EFCC ya ce daga bisani daraktan kudi ta majalisar ta bayyana bayan daskarar da asusunta na banki da aka yi.

Tsageru sun sheke DPO a Imo

'Yan bindiga da ake zargin tsagerun IPOB ne sun sheke CSP Fatmann Dooiyor. Dooiyor wanda shine babban jami'in dan sanda a Omuma, garinsu Gwamna Hope Uzodimma dake karamar hukumar Oru ta gabas dake jihar Imo.

Gagararrun 'yan bindiga sun tsinkayi babbar kotun tarayya dake Abuja inda aka gurfanar da Nnamdi Kanu. Jami'an DSS basu kai shi kotu ba, lamarin da yasa aka dage shari'ar zuwa watan Oktoba, Daily Trust ta wallafa.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Kwararrun likitocin Najeriya za su tsunduma yajin aiki

Kamar yadda takardar da mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Imo, CSP Mike Abattam ya fitar, yace 'yan sanda sun sheke shida daga cikin 'yan bindigan kuma an cafke 11 daga cikinsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel