'Yan sanda sun gayyaci Muhuyi yayin da majalisar Kano tayi watsi da umarnin kotu

'Yan sanda sun gayyaci Muhuyi yayin da majalisar Kano tayi watsi da umarnin kotu

  • Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta gayyaci tsohon shugaban hukumar PCACC, Muhuyi Magaji Rimingado
  • Kamar yadda majiya daga ofishin ta sanar, ana bukatar ya amsa tambayoyi kan rahoton lafiya na bogi da ya gabatarwa majalisar
  • Har ila yau, a zaman majalisar jihar na yau, 'yan majalisar sun bukaci a tsige shi, kama shi tare da gurfanar dashi gaban kotu

Kano

Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta gayyaci tsohon shugaban hukumar karbar korafi da yaki da rashawa na jihar Kano, PCACC, Muhuyi Magaji Rimingado, domin ya amsa wasu tambayoyi kan zargin yin rahoton asibiti na bogi.

Majiyoyi daga rundunar 'yan sandan ta sanar da Daily Nigerian cewa a halin yanzu Rimingado yana ofishin 'yan sanda dake Bompai domin amsa wasu tambayoyi.

KU KARANTA: Gwamnan Gombe na makokin manjon soja, matarsa da diyarsa da hatsari ya kashe

'Yan sanda sun gayyaci Muhuyi yayin da majalisar Kano tayi watsi da umarnin kotu
'Yan sanda sun gayyaci Muhuyi yayin da majalisar Kano tayi watsi da umarnin kotu. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Ku tsamo dukkan miyagun dake cikinku, Sarkin Muri ga shugabanni Fulani

Kara karanta wannan

Ku tsamo dukkan miyagun dake cikinku, Sarkin Muri ga shugabanni Fulani

Yayin da Rimingado ya amsa kiran 'yan sandan, majalisar jihar a ranar Litinin ta aminta da sallamar shi duk da umarnin da kotu ta bada na hana cigaba da tuhumarsa.

"Umarnin kotu a halin yanzu shine ta hana wadanda ake kara da su cigaba da bincikar wanda yayi kara ko su cigaba da aiwatar da wani al'amari mai alaka da hakan har sai ta kammala shari'ar," Kotun ta bada umarni.

A yayin yanke hukunci a zaman majalisa na yau, kwamitin mutum shida na majalisar da aka nada domin bincike kan mulkinsa daga 2015 zuwa 2021, ya bukaci a kama shi kuma a gurfanar dashi gaban kotu.

Majalisa ta gayyaci Rimingado

Idan zamu tuna, majalisar jihar Kano ta gayyaci Rimingado kuma ta bukaci ya bayyana a gaban kwamitin wucin-gadinta sakamakon korafin da aka kai a kansa na ranar Laraba, 14 ga watan Yulin 2021.

Amma yayin dogaro da rashin lafiya, Rimingado ya mika rahoton likita inda ya bukaci a bashi kwafin korafin kuma ya bukaci karin lokaci kafin ya bayyana a gaban majalisar.

Kara karanta wannan

Rimingado zai yi karar likitan da ya bashi shaidar asibiti ta bogi

A ranar 19, ga watan Yuli, asibitin kasa ya rubuta wasika ga majalisar jihar Kano inda suka ce wannan rahoton rashin lafiyar da ya bada na bogi ne, Daily Nigerian ta ruwaito.

A wani labari na daban, a ranar Lahadi ne hukumar ‘yan sandan jihar Kano ta musanta labaran da suka yi ta yawo akan harin da aka kaiwa tawagar sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero.

Labarai sun yi ta yawo akan yadda aka kaiwa tawagar sarkin hari akan hanyar Zaria zuwa Kano a ranar Lahadi, Kamar yadda Daily Trust ta wallafa.

Saidai Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce hatsari ne ya auku da motar karshen tawagar sarkin ba wai hari aka kaiwa sarkin ba.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel