Gwamnan Gombe na makokin manjon soja, matarsa da diyarsa da hatsari ya kashe

Gwamnan Gombe na makokin manjon soja, matarsa da diyarsa da hatsari ya kashe

  • Gwamnatin jihar Gombe ta fada alhinin mutuwar Manjo Auwal Danbabu Mohammed, matarsa da diyarsa
  • An gano cewa mummunan hatsarin mota ya ritsa da sojan a kan babbar hanyar Zamfara zuwa Kano
  • Gwamnan ya samu rakiyar mukarrabansa da suka hada da kwamishinoni wurin ta'aziyya ga iyalansa

Mummunan alhini ya fada jihar Gombe yayin da wani Manjo Auwal Danbabu Mohammed, matarsa Fadila Auwalu Shehu Brema da diyarsa Aisha suka rasa rayukansu yayin wani mummunan hatsarin mota dasuka gwabza.

Gwamnan jihar, Muhammad Inuwa Yahaya ya samu labarin mai cike da alhini kuma ya kwatanta shi babban rashi ga jihar da jama'ar jihar.

Hatsarin ya faru ne a kan babban titin Zamfara zuwa Kano yayin da iyalan suke kan hanyar komawa sansaninsa bayan shagalin sallah, tribune online ta ruwaito.

KU KARANTA: Da duminsa: Kotu a Kano ta haramtawa majalisar jiha binciken Rimingado

Gwamnan Gombe na makokin manjon soja, matarsa da diyarsa da hatsari ya kashe
Gwamnan Gombe na makokin manjon soja, matarsa da diyarsa da hatsari ya kashe. Hoto daga tribuneonlineng.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Rashin tashin bam ko 1 yayin sallah alamace ta dawowar ingancin tsaro, Fadar Buhari

Kara karanta wannan

Karo na farko, Ganduje ya yi magana kan lamarin AbdulJabbar Kabara

Har zuwa lokacin rasuwarsa, Manjo Auwal Danbabu yana aiki ne da birged ta 1 ta rundunar sojin kasa dake Gusau a jihar Zamfara, tribune online ta wallafa.

A ranar Juma'a da ta gabata, Gwamna Inuwa Yahaya ya jagoranci tawagar ta'aziyya zuwa gidan Alhaji Shehu Brema dake Kumbiya-Kumbiya inda ya jajanta musu kan wannan babban rashi.

Ya jajanta tare da bayyana cewa rahsin masoya babban abun alhini ne. Gwamnan ya ce, "Rashin matashi a irin wannan shekarun yana kawo alhini ballantana ga 'yan uwa da abokan arziki."

"Muna makoki a madadin gwamnati da jama'ar jihar Gombe, muna ta'aziyya tare da fatan Allah ya basu hakurin jure wannan rashin kuma ya bashi Aljannar Firdaus," gwamnan ya sanar da iyalan.

Gwamnan ya samu rakiyar shugaban ma'aikata, Alhaji Abubakar Inuwa Kari, shugaban ma'aikatan gwamnati, Alhaji Baayo Yahaya, kwamishinoni da sauransu.

A wani labari na daban, hukumar ‘yan sandan jihar Katsina ta bankado harin da ‘yan bindiga suka kai karamar hukumar Batsari dake jihar.

Kara karanta wannan

Matashi daga jihar Kano zai tsaya takarar shugaban kasa a APC, ya gana da manya kan batun

Kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito, Kakakin hukumar na jihar, SP Gambo Isah ne ya bayyana hakan a wata takarda ta ranar Juma’a.

A cewarsa: “A ranar Juma’a, 23 ga watan Yulin 2021 da misalin karfe 2:30, ‘yan bindiga suka rufe hanyar Jibia zuwa Batsari daidai kauyen Kabobi dake karamar hukumar Batsari da baburansu dauke da bindigogi kirar AK 47."

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel