Majalisar a Zamfara ta nemi matamakin gwamna ya bayyana a gabanta cikin sa'o'i 48

Majalisar a Zamfara ta nemi matamakin gwamna ya bayyana a gabanta cikin sa'o'i 48

  • Majalisar dokokin jihar Zamfara ta nemi ganin mataimakin gwamnan jihar cikin gaggawa
  • Majalisar ta bayyana cewa, tana son ganin Barista Aliyu Mahdi Gusau cikin kasa da sa'o'i 48
  • Majalisar ta bayyana dalilin da yasa take son ganin mataimakin gwamnan cikin gaggawa

Majalisar Dokokin Jihar Zamfara ta ba Mataimakin Gwamna, Barista Aliyu Mahdi Gusau, wa’adin sa'o'i 48 ya bayyana a gabanta kan zargin aikata ba daidai ba a hukumance, Channels Tv ta ruwaito.

Zai bayyana a gaban majalisar ne kan wani taron siyasa da aka gudanar a ranar 10 ga watan Yuli, yayin da 'yan bindiga suka kai hare-haren kan al'ummomin Maradun a daidai lokacin da ake taron.

Karin wa’adin ranar Talatan ya biyo bayan kudirin da Mataimakin Shugaban majalisar, Nasiru Bello Bungudu ya gabatar don bayyana dalilin da ya sa ya gudanar da taron siyasa a yayin da kashe-kashen da suka faru a jihar.

Majalisar jihar Zamfara ta nemi matamakin gwamna ya zo gabanta cikin sa'o'i 48
Kakakin majalisar jihar Zamfara, Nasiru Magarya | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Mataimakin shugaban ya gabatar da kudirin a karkashin bayanan kashin kansa da kuma kudurin majalisar sannan Hon Shafi’u Dama Wanke mai wakiltar mazabar Gusau II ya goyi bayansa.

Kara karanta wannan

Gaisuwar Sallah: Wasu ‘Yan Majalisar Tarayya da Gwamnoni 11 sun ziyarci Garin Daura

Wani bangare na bayanin kan kudurin kamar yadda kakakin majalisar, Mustapha Jafaru ya fitar, ya ce:

“Bayan lura da kyau game da bukatar da mataimakin shugaban majalisa ya gabatar, kakakin majalisa Nasiru Mu’azu Magarya ya yi magana da takwarorinsa kan ko sun amince su tsawaita wa’adin awanni 48 ga mataimakin gwamnan ya bayyana a gaban majalisar? Mambobin sun amince baki daya ta hanyar kuri’ar.”

Kotu ta dakatar da shirin tsige mataimakin gwamnan jihar Zamfara

Wata babbar kotun tarayya dake Abuja ta bayar da umarnin hana majalisar dokokin jihar Zamfara tsige mataimakin gwamnan jihar, Mahdi Aliyu Gusau.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa kotun ta bayar da wannan umarni ne a ranar Litinin, 19 ga watan Yuli, bayan duba karar da Ogwu James Onoja ya shigar a madadin jam’iyyar PDP.

A wani bangare na umarnin, Mai shari’a Obiora Egwuatu ya kuma sake gargadi gwamnan jihar Zamfara da babban alkalin jihar kan ci gaba da shari’a dangane da duk wani shirin tsige Mahdi Gusau.

Kara karanta wannan

Kano: An sauke shugaban makaranta saboda ya bai wa dalibai hutun Sallah

Onoja ya fadawa kotu cewa majalisar dokoki da wasu na shirin tsige mataimakin gwamnan, saboda kin sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

Lauyoyin sun ce ya zama dole ga kotu ta shiga tsakani game da batun ta hanyar bayar da dakatarwar wucin gadi ga wadanda ke shirin tsige shi.

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa a hukuncin da alkalin ya yanke ya ce ya gamsu da cewa lamari ne mai bukatar matukar gaggawa dake bukatar stoma bakin kotu.

Sannan ya umarci bangarorin da su ci gaba da kasancewa yadda suke har zuwa lokacin da za a saurari karar da mai shigar da kara ya shigar.

"Ka kiyaye ni," Gwamnan Zamfara ya gargadi mataimakinsa

A wani labarin, Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle, a ranar Asabar ya ce ba zai yarda da halin rashin ladabi daga mataimakinsa, Mahdi Aliyu ba, rahoton PremiumTimes.

Matawalle ya fusata ne kan wani taron siyasa da aka yi kwanan nan wanda mataimakin gwamnan ya yi domin sake jaddada biyayyarsa ga jam’iyyar hamayya ta PDP.

Kara karanta wannan

Dalilin da yasa farashin kayan Masarufi yayi tashin gwauron zabi, Shugaba Buhari

Dukkansu sun shigo gwamnati ne a matsayin ‘yan takarar jam’iyyar PDP amma Matawalle da kusan dukkanin zababbun shugabanni a jihar a watan da ya gabata, sun sauya sheka zuwa Jam’iyyar APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel