Gaisuwar Sallah: Wasu ‘Yan Majalisar Tarayya da Gwamnoni 11 sun ziyarci Garin Daura
- Femi Gbajabiamila da abokan aikinsa sun kai wa shugaban kasa ziyara a Daura
- Gwamnonin jihohi fiye da 10 sun je garin Daura, sun taya Buhari murnar sallah
- Daga cikin gwamnonin da suka kai ziyara akwai gwamnonin Kano da na Katsina
'Yan Majalisa sun je yi wa Buhari yawon sallah
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin shugaban majalisar wakilan tarayya, Rt. Hon. Femi Gbajabiamila da wasu ‘yan majalisa.
Jaridar The Cable ta ce shugaban kasar ya gana da ‘yan majalisar ne a gidansa da ke garin Daura, jihar Katsina, a ranar Alhamis, 22 ga watan Yuli, 2021.
Femi Gbajabiamila da sauran tawagarsa sun je har garin na Daura ne domin su taya mai girma shugaban kasa bikin babbar idin da aka yi a ranar Talata.
A cikin ‘yan rakiyar Gbajabiamila, akwai shugaban masu rinjaye a majalisa Honarabul Alhassan Ado Doguwa, mai wakiltar Doguwa da Tudun-Wada.
Rahoton ya ce shugaba Muhammadu Buhari ya rika karbar bakuncin ‘yan siyasa dabam-dabam yayin da ya zo yin hutun sallah a mahaifarsa ta Daura.
Daga cikin wadanda su ka hadu da shugaban kasar akwai manyan ‘yan siyasan Zamfara. Hakan na zuwa kwanaki kadan bayan APC ta yi kamu a jihar.
Hotunan da Buhari Sallau ya fitar, sun nuna shugaban kasar ya yi hoto tare da ‘yan siyasan Zamfara da gwamna Muhammad Bello Matawalle ya jagoranta.
Kamar yadda rahotanni su ka zo mana, Muhammadu Buhari ya zauna da wasu daga cikin gwamnonin APC da su ka baro jihohinsu, su ka ziyarce sa.
Daga cikin gwamnonin akwai Kayode Fayemi, Aminu Bello Masari, Simon Bako Lalong, Abdullahi Sule, Abubakar Bello, da kuma Gboyega Oyetola.
Sauran gwamnonin sun hada da Abdullahi Umar Ganduje, Ben Ayade, David Umahi, da Inuwa Yahaya.
A baya kun ji cewa tulin dukiyar hadimin Diezani Alison-Madueke, Jide Omokore, ya tara su na neman zama mallakar Najeriya yayin da ya koma kotu da EFCC.
Omokore zai iya rasa wasu daga cikin dukiyoyi, gidaje da kudin da ya tara a banki. Alkali ya ba hukumar EFCC dama ta rike dukiyoyin na-kusa da tsohuwar Ministar.
Asali: Legit.ng