Dalilin da yasa farashin kayan Masarufi yayi tashin gwauron zabi, Shugaba Buhari

Dalilin da yasa farashin kayan Masarufi yayi tashin gwauron zabi, Shugaba Buhari

  • Shugaba Buhari ya taya yan Najeriya murnar babbar Sallah
  • Shugaban kasan ya tabbatarwa yan Najeriya gwamnatinsa zata cigaba da kokari
  • Yau ranar Sallar Eidul-Adha wacce aka fi sani da Sallar Layya

Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Litnin ya yi jawabi game tashin farashin kayan masarufi a Najeriya duk da kudin da gwamnatinsa ke zubawa cikin aikin noma.

Buhari ya bayyana hakan ne a sakon barka da Sallan da ya aikewa yan Najeriya, wanda mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu, ya saki a Abuja.

Shugaban kasan ya tabbatar da cewa gwamnatinsa na iyakan kokarinta wajen magance hauhawar farashin kayan Masarufi da annobar COVID-19 da matsalar tsaro suka haddasa.

A sakon, Buhari ya bayyana cewa ambaliyar ruwan sama tayi sanadiyar lalacewar gonaki da dama kuma hakan ya illata samar da kayan abinci.

Shugaba Buhari
Dalilin da yasa farashin kayan Masarufi yayi tashin gwauron zabi, Shugaba Buhari Hoto: Presidency
Asali: Twitter

Yace:

"A tarihin kasar nan babu gwamnatin da ya zuba kudi da yawa aikin noma kamar yadda mukeyi domin noman kayan Masarufi kimanin 20, ta hanyar bayar da basussuka da taimako ga manoma."

Kara karanta wannan

Badaru Ya Buƙaci Musulmi Su Yi Addu’a Domin Kawo Ƙarshen Rashin Tsaro

"A matsayina na zababben shugaban da ya samu goyon bayan gama-garin jama'a, ina tabbatar muku da cewa zamu cigaba da amfani da hanyoyin kawowa yan Najeriya sauki, wanda ya hhada samar da takin zamani cikin farashi mai rahusa."

Shugaban kasan ya kara da cewa bayan ambaliyar da ta lalata gonakin shinkafa, wasu yan kasuwa ke iyawa yan Najeriya zagon kawa.

A cewar Buhari, hakazalika matsalar tsaro ta yiwa harkar noma mumunan illa saboda manoma basu iya zuwa gona saboda yan bindiga da yan ta'adda.

Asali: Legit.ng

Online view pixel