Na gwammace in mutu da na bai wa Fulani filin kiwo, in ji wani Gwamna

Na gwammace in mutu da na bai wa Fulani filin kiwo, in ji wani Gwamna

  • Gwamnan jihar Benue ya bayyana karara cewa, ya gwammace ya mutu kan mika fili a jiharsa ga Fulani
  • Gwamnan ya bayyana haka ne yayin da yake koka wa kan yadda lamurran ta'addanci ke ta'azzara a jiharsa
  • Gwamnan ya kuma zargi gwamnatin shugaba Buhari da goya wa Fulani baya wajen aikata ta'addanci

Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, a karo na goma sha biyar ya zargi gwamnatin tarayya da yin sakaci a yakin da take da rashin tsaro, AIT ta ruwaito.

Gwamna Ortom, wanda ya bayyana hakan a Makurdi lokacin da yake karbar bakuncin likitocin agaji ya ce gwamnatin tarayya na da karfin da za ta iya kama makiyaya amma ta zabi bin wata hanyar don cimma burinta na tsarkake kabilanci.

Gwamnan na Jihar Benue ya nace cewa ya gwammace ya mutu akan ya ba da filayensa ga Fulanin da suka yi waje da sama da miliyan da na mazauna jihar daga muhallinsu.

Kara karanta wannan

Ka Ƙyalle Buhari Ya Wataya: Ƙungiyar Tibi Ta Faɗa Wa Gwamnan Benue Samuel Ortom

Na gwammace in mutu da na bai wa Fulani filin kiwo, in ji Gwamna
Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Ya kara da cewa yawan mace-macen da ke karuwa daga barnar wasu makiyaya masu kashe mutane ya zama abin tsoro kamar yadda alkaluman yau da kullun suka nuna.

Gwamnan ya sha alwashin cewa a shirye yake da ya mutu akan ya kyale a bai wa makiyaya wani yanki a jihar, in ji Sahara Reporters.

A kalamansa, cewa ya yi:

"Wadannan 'yan ta'addanp, sun nuna kansu a shafukan sada zumunta, suna ikirarin sun zo ne domin wata manufa ta korar mutanenmu da kwace filayensu da kashe su.
"Kuma a nan suna samun goyon bayan Gwamnatin Tarayya amma a wurina, idan suka zo, to a shirye nake in mutu fiye akan in mika filayena ga Fulani. Idan Allah bai kare ni ba, to ba ni bukatar taimako daga kowa."

Sarki a arewacin Najeriya ya ba Fulani makiyaya wa'adin kwanaki 30 su bar jiharsa

Sarkin masarautar Muri a jihar Taraba, Abbas Tafida ya ba da wa’adin kwanaki 30 ga makiyaya da ke addabar mazauna jihar kan su bar dazuzzukan fadin jihar ko kuma a tilasta musu yin hakan.

Kara karanta wannan

Ku Tona Min Asiri Idan Har Na Saci Kuɗin Talakawa, Gwamnan Nigeria Ya Faɗa Wa Masu Zarginsa

Gidan talabijin na Channels ta ce, Sarkin ya bayar da wa'adin ne a ranar Talata bayan sallar Idi. Wannan ya biyo bayan yawaitar sace-sacen mutane, kashe-kashe, da hare-hare a jihar da wasu miyagu da ake zargin makiyaya ne ke aikatawa.

Ya yi ikirarin cewa Fulani makiyaya ne ke da alhakin aikata laifuka a jihar don haka ya kamata su bar dazuzzukan da ke cikin jihar cikin kwanaki 30 ko kuma a tilasta musu fita.

Dillalan shanu na neman filin kiwo mai girman murabba'in mita 30000 a wata jihar kudu

A wani labarin daban, A jiya ne Kungiyar Dillalan Shanu na Delta ta nemi fili mai fadin muraba'in mita dubu 30 a cikin kananan hukumomi 25, a matsayin wuraren da za a ware domin kiwo da kasuwancin shanu, The Nation ta ruwaito.

Kungiyar ta bayyana haka ne a Asaba, babban birnin jihar Delta, yayin sauraran ra’ayoyin jama’a game da wata doka da za ta tanadi Dokar Kiwo da kasuwancin shanu da Haramta kiwo sakaka da kuma lamurran da suka shafi jihar.

Kara karanta wannan

Mutumin da ya yi yunkurin kashe shugaban kasar Mali ranar sallah ya mutu a magarkama

Jawabin wanda kwamitin hadin gwiwa na majalisar dokokin jihar Delta kan kudade na musamman da kuma na Noma da albarkatun kasa suka shirya, ya sami kusan tunatarwa 12 daga hukumomin gwamnatin jihar da masu ruwa da tsaki a harkar kasuwancin dabbobi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel