Dillalan shanu na neman filin kiwo mai girman murabba'in mita 30000 a wata jihar kudu

Dillalan shanu na neman filin kiwo mai girman murabba'in mita 30000 a wata jihar kudu

  • Kungiyar dillalan shanu a jihar Delta sun nemi gwamnati ta basu filin kiwo mai matukar girma
  • Sun bayyana haka ne saboda su samu damar gamsar da jihar wajen samar da kiwo mai inganci
  • Sun nemi akalla murabba'in mita 30,000 na kiwo da kasuwancin shanu a fadin jihar ta Delta

A jiya ne Kungiyar Dillalan Shanu na Delta ta nemi fili mai fadin muraba'in mita dubu 30 a cikin kananan hukumomi 25, a matsayin wuraren da za a ware domin kiwo da kasuwancin shanu.

Kungiyar ta bayyana haka ne a Asaba, babban birnin jihar Delta, yayin sauraran ra’ayoyin jama’a game da wata doka da za ta tanadi Dokar Kiwo da kasuwancin shanu da Haramta kiwo sakaka da kuma lamurran da suka shafi jihar.

Jawabin wanda kwamitin hadin gwiwa na majalisar dokokin jihar Delta kan kudade na musamman da kuma na Noma da albarkatun kasa suka shirya, ya sami kusan tunatarwa 12 daga hukumomin gwamnatin jihar da masu ruwa da tsaki a harkar kasuwancin dabbobi.

Kara karanta wannan

Dalilai da ke nuna alamun Nnamdi Kanu na iya fuskantar hukuncin kisa ko daurin rai da rai

Dillalan shanu na neman filin kiwo mai girman murabba'in mita 30000 a wata jihar kudu
Taswirar jihar Delta | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: Twitter

Takardar yarjejeniyar kungiyar, wacce Shugaban kungiyar, Alhaji Musa Shuwa ya sanya wa hannu, ta ce, murabba'in mita 5,000 da aka ware a matsayin wuraren kiwo ya yi matukar karanci saboda wuraren da ake sa ran za su kasance a yankunan.

Shuwa ya ce a halin yanzu, kungiyar tana kula da kasuwar dabbobi (shanu) a garuruwa bakwai a cikin jihar, sannan ta kara da cewa mafi kankanta ya kasance a wani yanki da yakai kimanin murabba'in mita 4,500, yayin da mafi girma shine kimanin murabba'in mita 7,000.

Jaridar The Nation ta ruwaito Shuwa na cewa:

“Wannan kawai na kasuwanni ne. Hakanan, kowace kasuwa tana daukar kasa da shanu 800 a kowane mako. Da wuya membobinmu su sayar da shanunsu duka a kasuwa, saboda haka akwai bukatar ciyar da shanun ta hanyar kiwo.

Bayan bayyana hujjojinsu, sun nemi gwamnati ta amince da karin filin kiwon da ya kai kimanin murabba'in mita 30,000, a cewarsu:

Kara karanta wannan

Gwamna Masari na Katsina ya bayyana mafita ga matsalar rashin tsaron Najeriya

“Don haka, muna bayar da shawarar cewa domin gamsar da samun mayankan dabbobi, asibitin dabbobi, kasuwar dabbobi, ofishin gudanarwa da kuma ofishin tsaro kamar yadda aka bayar a Sashe na 2 (b) zuwa (g), Sashe na 2 (a) ya kamata a sanar da cewa yankin da aka kebe zai kunshi mafi karancin fili mai murabba'in mita 30,000."

Sarki a arewacin Najeriya ya ba Fulani makiyaya wa'adin kwanaki 30 su bar jiharsa

Sarkin masarautar Muri a jihar Taraba, Abbas Tafida ya ba da wa’adin kwanaki 30 ga makiyaya da ke addabar mazauna jihar kan su bar dazuzzukan fadin jihar ko kuma a tilasta musu yin hakan.

Gidan talabijin na Channels ta ce, Sarkin ya bayar da wa'adin ne a ranar Talata bayan sallar Idi.

Wannan ya biyo bayan yawaitar sace-sacen mutane, kashe-kashe, da hare-hare a jihar da wasu miyagu da ake zargin makiyaya ne ke aikatawa.

Kara karanta wannan

Buhari ya yi alkawarin kawo karshen ta’addanci a arewa - Matawalle

Ya yi ikirarin cewa Fulani makiyaya ne ke da alhakin aikata laifuka a jihar don haka ya kamata su bar dazuzzukan da ke cikin jihar cikin kwanaki 30 ko kuma a tilasta musu fita.

An yi luguden wuta tsakanin 'yan fasa-kwaurin shinkafar waje da jami'an kwastam

A wani labarin, Akalla jami'an Kwastam uku da wani soja sun ji rauni lokacin da wasu masu fasa kwauri suka far musu a yankin Igboora da ke karamar hukumar Ibarapa ta jihar Oyo a ranar Juma'a.

Theophilus Duniya, Jami’in Hulda da Jama’a na Kwastam, sashin Ayyuka na Tarayya, shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar kuma ya ba manema labarai a Ibadan, Daily Nigerian ta ruwaito.

Mr Duniya ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 8:00 na daren Juma'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.