Ka Ƙyalle Buhari Ya Wataya: Ƙungiyar Tibi Ta Faɗa Wa Gwamnan Benue Samuel Ortom

Ka Ƙyalle Buhari Ya Wataya: Ƙungiyar Tibi Ta Faɗa Wa Gwamnan Benue Samuel Ortom

  • Kungiyar matasan Tibi a jihar Benue ta bukaci Gwamna Samuel Ortom ya kyalle Shugaba Buhari
  • Kungiyar ta ce gwamnan ba shi da aikin yi sai furta maganganu na sukar shugaban kasa yayin da shi kuma ya ke musgunawa masu sukarsa a jiha
  • Kungiyar da shawarci Gwamna Ortom ya mayar da hankali wurin warware rikice-rikice da dama a jiharsa da samarwa mutane abin more rayuwa

Makurdi, Benue - Kungiyar Matasan Tibi ta yi kira ga Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue ya mayar da hankali kan samar da mulki na gari ga mutanen jiharsa a maimakon bata lokaci da sunan sukar Shugaba Muhammadu Buhari, rahoton Daily Trust.

Kungiyar ta Tiv Youth Council Worldwide ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da shugabanta, Hon Mike Msuaan ya fitar.

Ka Ƙyalle Buhari Ya Wataya: Ƙungiyar Tibi Ta Faɗa Wa Gwamnan Benue Samuel Ortom
Shugaba Muhammadu Buhari da Gwamna Samuel Ortom. Hoto: The Nation
Asali: Facebook

Daily Trust ta ruwaito Musuaan ya ce bai san dalilin da yasa gwamnan ke gaggawar neman abin da zai hada shi da shugaban kasa ba don jaridu su dauka a yayin da akwai ayyuka da dama na gwamnati da ke bukatar kulawansa a jiharsa.

Kara karanta wannan

Buhari ga 'yan siyasa: Kada ku yi amfani da ni wurin yaudarar masu saka kuri'a

Kungiyar ta matasan na Tibi ta bayyana zargin da gwamnan ke yi wa Shugaba Buhari a matsayin 'munafinci da ya kai girma na ban mamaki'.

A cewar kungiyar:

"Abin mamaki ne ganin gwamnan da ya ke amfani da karfin ikonsa a jiha wurin razana wadanda ke sukarsa bisa rashin iya samarwa mutanen Benue kayayyakin more rayuwa zai juya ya zargi shugaban kasa da yi wa masu sukarsa barazana.
"Muna sa ran ganin gwamnan ya mayar da hankali wurin warware matsala kashe-kashen da yan daba ke yi kananan hukumomin Katsina-Ala, Ukum da Logo a jihar rikicin garuruwa a Bonta, karamar hukumar Konshisha da Oju wanda ya janyo asarar rayyuka da biliyoyin naira.
"Rikicin da ake cigaba da yi tsakanin garuruwan Ipiav da Yandev a karamar hukumar Gboko da sauran rikice-rikice sun isa saka gwamna ya natsu ya yi aiki."

El-Rufai zai sake yi wa malaman makaranta jarrabawar gwaji a Kaduna

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya gwangwaje sojojin da suka ji rauni da miliyoyin Nairori ranar Sallah

A wani labarin daban, gwamnatin jihar Kaduna ta ce za ta sake yi wa malaman makarantun frimare gwajin sanin makamashin aiki a yunkurinta na tabbatar da samar da ilimi mai inganci a makarantun, The Punch ta ruwaito.

Mohammed Mubarak, Mamba na dindindin, Sashin Sanya Ido Kan Ayyuka, Hukumar Kula da Makarantun Frimare na jihar Kaduna ne ya sanar da hakan yayin tattaunawa da manema labarai a Kaduna a ranar Laraba, rahoton Today NG.

Mubarak ya ce gwamnatin jihar, a 2017 ta sallami kimanin malamai 22,000 da ba su cancanta ba daga makarantun frimari domin sun fadi jarrabawar gwada sanin makamashin aiki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164