Ku Tona Min Asiri Idan Har Na Saci Kuɗin Talakawa, Gwamnan Nigeria Ya Faɗa Wa Masu Zarginsa

Ku Tona Min Asiri Idan Har Na Saci Kuɗin Talakawa, Gwamnan Nigeria Ya Faɗa Wa Masu Zarginsa

  • Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma ya bibiyi ayyukan da gwamnatinsa ta yi a shekarar da ta gabata
  • Uzodinma ya ce ya yi taron masu ruwa da tsaki ne domin sanar mutanen jihar abin da gwamnatinsa ta yi
  • Gwamnan ya yi wa mutanen jiharsa alkawarin cewa gwamnatinsa za ta cigaba da habbaka gine-gine a jihar

Owerri, Jihar Imo - Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo ya ce bai taba satar kudin al'umma ba tun lokacin da ya kama aiki a matsayin gwamna a jiharsa.

The Nation ta ruwaito cewa a ranar Asabar 24 ga watan Yuli, gwamnan ya kallubalanci mutanen jihar su fallasa shi idan ya taba karkatar da kudaden al'umma.

Ku Tona Min Asiri Idan Har Na Saci Kuɗin Talakawa, Gwamnan Nigeria Ya Faɗa Wa Masu Zarginsa
Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma. Hoto: The Nation
Asali: Facebook

An ruwaito cewa ya yi wannan furucin ne a yayin taron masu ruwa da tsaki a Owerri.

Uzodinma ya ce a shirye ya ke ya amince a bincike shi domin ya nuna cewa bai yi almubazaranci da kudin al'umma ba.

Kara karanta wannan

Mutumin da ya yi yunkurin kashe shugaban kasar Mali ranar sallah ya mutu a magarkama

Ya ce ya zama gwamna ne domin ya yi wa mutane hidima ba tara dukiya ba.

Gwamnan ya ce:

"Kamar yadda na ke karbo kayayyakin al'umma jihar Imo daga hannun wadanda suka kwace kayan suka mayar nasu, nima idan na sauka za a bincike ni.
"Shi yasa na ke son sake jadada wa a gabanku cewa ban zama gwamna domin in fi jiha ta kudi bayan na sauka mulki ba, sai dai domin in yi muku hidima cikin tsoron Allah. Don haka, ba zan yi kasa a gwiwa ba wurin karbo arzikin jihar Imo da aka sace."

A cewar Vanguard, Uzodinma ya bayyana cewa gwamnatinsa ta gwangwaje jihar Imo da tituna.

Ya bayyana cewa a baya-bayan nan gwamnatinsa ta gyara kimanin tituna 42 a sassan jihar cikin shekarar da ta gabata.

Shugaban CAN ya jinjinawa gwamnan Imo

A wani labarin daban, Samson Ayokunle, shugaban kungiyar kirista ta Nigeria, CAN, ya bayyana Uzodinma a matsayin gwamnan mai yin ayyukan ban mamaki, The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

A gaskiya Gwamna Ganduje ya na mana shisshigi a shari’ar Abduljabbar Kabara inji Lauyoyinsa

Ya bayyana hakan ne yayin da ya ke jawabi da dubban kiristoci a wurin wani taron addua da CAN reshen jihar Imo ta shirya a Hero's Square, Owerri.

A cewarsa, ikon Allah ne yasa Uzodinma ya zama gwamnan jihar. Ya yi kira ga gwamnan ya rika kusantar Allah kafin daukan matakai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel