Mutumin da ya yi yunkurin kashe shugaban kasar Mali ranar sallah ya mutu a magarkama

Mutumin da ya yi yunkurin kashe shugaban kasar Mali ranar sallah ya mutu a magarkama

  • Mutumin da ya yi kokarin daba wa shugaban kasar Mali wuka ya mutu a magarkama
  • Rahoto daga kasar ya bayyana yadda lamarin ya faru, duk da cewa ba a bayyana musabbabin mutuwarsa ba
  • A ranar babbar sallah ne wani mutum ya yi kokarin daba wa shugaban kasar ta Mali wuka a masallaci

Kasar Mali - Mutumin da ake zargi da kokarin kashe shugaban soja mai karfin iko Assimi Goita, wanda ya kitsa juyin mulki sau biyu a kasa da shekara guda, ya mutu a tsare, in ji gwamnati a ranar Lahadi, 25 ga watan Yulin 2021.

Wanda ake zargin da ba a bayyana ainihinsa ba, an tsare shi bayan yunkurin kisan gillar da ya yi a Babban Masallacin Bamako ranar Talata, Channels Tv ta ruwaito.

"A lokacin bincike...lafiyarsa ta tabarbare" daga nan aka kwantar da shi a asibiti, amma "kash, ya mutu," in ji gwamnati a cikin wata sanarwa.

Mutumin da ya yi yunkurin kashe shugaban kasar Mali ranar sallah ya mutu a magarkama
Shugaban kasar Mali | Hoto: aljazeera.com
Asali: UGC

Sanarwar ta kara da cewa, nan take aka bayar da umarnin gudanar da bincike kan musabbabin mutuwar mutumin.

Wani mutum ya yi yunkurin kashe shugaban kasar Mali ranar babbar Sallah

Wani mutum dauke da wuka ya afka wa Goita bayan Sallar idi a ranar Talata, a cewar wani wakilin AFP a wurin.

Jami'an tsaron Goita sun yi gaggawar kare shi, sannan daga baya ya bayyana a gidan Talabijin din kasar yana cewa yana nan “lafiya lau”, yana mai Allah wadai da harin.

Aljazeera ta ruwaito shugaban na cewa:

"Wannan wani bangare ne na kasancewa jagora, ko yaushe akwai rashin wadatar zuci."
"Akwai mutanen da a kowane lokaci ke son gwada abubuwa don haifar da rashin zaman lafiya."

Maharin, matashi mai sanye da wando da farar riga, an kama shi a wurin kuma jami’an leken asiri na Mali sun tafi da shi.

Ba a gabatar da wanda ake zargin ga hukumomin shari'a ba, in ji wata majiya da ta nemi a sakaya sunan ta a ranar Lahadi.

Ba a bayyana ko wanene ba, amma kwamishina Sadio Tomoda ya fada a yammacin Talata cewa shi malamin makaranta ne, ba tare da yin karin bayani ba.

Masu gabatar da kara sun bukaci bincike kan lamarin.

A ranar Lahadi, gwamnati ta ce mutuwar wanda ake zargin ba wani cikas ba ne ga ci gaba da bincike, yayin da ta kara da cewa:

"Musamman tunda hujjoji na farko da bayanan sirri da aka tattara sun nuna cewa shi ba daga wani bangare ba ne".

Yadda 'yan Boko Haram suka kai hari sansanin sojojin Kamaru

A wani labarin, Mayakan Boko Haram sun mamaye wani sansanin sojoji a yankin Arewa mai nisa na Kamaru a ranar Asabar 24 ga watan Yuli, 2021, inda suka kashe a kalla sojoji bakwai tare da jikkata wasu da dama, in ji majiyar sojoji wasu da daban.

Sun buge sansanin da ke yankin Sagme da misalin karfe 4.00 na safiyar ranar Asabar, kamar yadda sojoji biyu da wani mazaunin yankin suka shaida wa Xinhua.

Maharan, wadanda ke dauke da muggan makamai, wasu daga cikinsu cikin shigar sojoji sun zo ne cikin jerin gwanon motoci shida, in ji wani soja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel