Buhari ya yi alkawarin kawo karshen ta’addanci a arewa - Matawalle
- Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle, ya bayyana cewa Shugaba Buhari ya sha alwashin kawo karshen ta'addanci a yankin arewa
- Matawalle ya jadadda cewa gwamnonin yankin sun sanar da shugaban kasar halin da suke ciki a yayin ganawar da suka yi
- Ya kuma yi kira ga masu ruwa da tsakia kan su hada kai domin kawo karshen kalubalen da kasar ke ciki
Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ya yi alkawarin kawo karshen rashin tsaro a arewa.
Gwamnan ya fadi haka ne a wata sanarwa da shi da kan sa ya sanya wa hannu, jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Matawalle ya ce yayin ganawa da shugaban kasa, gwamnoni daga jihohin arewa sun yi ta bayyana halin da suke ciki, abubuwan da suke fata daga gwamnati, da kuma kokarin samar da mafita mai dorewa.
Ya ce gwamnonin arewa sun dukufa wajen tallafawa kokarin shugaban kasa na kawo karshen matsalolin tsaro a kasar.
Matawalle ya yi kira ga fitattun mutane da sauran ‘yan siyasa, musamman daga arewacin Najeriya, da su kasance masu hadin kai tare da fuskantar kalubalen da ke lalata ci gaban yankin da ci gaban sa.
"Shugaban kasar ya ba da tabbacin cewa zai kawo karshen matsalar tare da mayar da yankin da kuma kasar baki daya ga abubuwan da suka rasa.
“Lokaci ya yi da zamu kawo karshen barna da kashe-kashe, mu koyi halaryar yafewa laifinmu, mu nisanci rarrabuwar kawuna sannan mu zama masu hadin kai.
“Za mu ci gaba da mai da hankali ga ci gaban kasa tare da yin watsi da banbancin siyasa ba tare da la’akari da jam’iyyar da muke ciki ba,” inji shi.
Matawalle ya yi kira ga shugabanni da su ci gaba da jan hankulan mutane game da hanyoyin da suka dace da kuma ci gaban kasar, Jaridar The Cable ta ruwaito.
"Dole ne shugabanni su yi shawarwari kan mafita, su guji son kai don kawo karshen kashe-kashe da barnata dukiya.
"Tawaye, musamman a arewa maso gabas da sauran ayyukan 'yan fashi, sun kawo cikas ga ayyukan tattalin arziki, ilimi, noma da sauran ayyukan zamantakewa a arewacin Najeriya," in ji shi.
A wani labari na daban, wani mutum a Katsina, Yahuza Ibrahim, wanda ya sanya wa diyarsa suna Buhariyya, watakila takwararar Shugaba Muhammadu Buhari, ya canza sunanta zuwa Kauthar.
Ya ce ya yi hakan ne saboda shugaban kasar ya gaza cika alkawuran da ya dauka yayin yakin neman zabe.
A wani faifan bidiyo da Legit ta samu ta gani, Mista Ibrahim, wanda ya fito daga Karamar Hukumar Jibia da ke cikin Jihar Katsina, ya ce yadda a da yake ganin kimar Buhari ya sa ya sanya wa ‘yarsa suna “Buhariyya ”.
Asali: Legit.ng