Dan Katsina ya yi bikin canza sunan diyarsa daga Buhariyya zuwa Kausar, ya ce Shugaban Kasar ya gaza

Dan Katsina ya yi bikin canza sunan diyarsa daga Buhariyya zuwa Kausar, ya ce Shugaban Kasar ya gaza

  • Wani tsohon masoyin Buhari ya sauya wa diyarsa suna daga Buhariya zuwa Kausar
  • Ya ce a da can Shugaban yana da alkibla amma yanzu ya rasa kimarsa
  • A cewarsa Buhari ya gaza cika alkawuran da ya dauka yayin neman zabe

Wani mutum a Katsina, Yahuza Ibrahim, wanda ya sanya wa diyarsa suna Buhariyya, watakila takwararar Shugaba Muhammadu Buhari, ya canza sunanta zuwa Kauthar.

Ya ce ya yi hakan ne saboda shugaban kasar ya gaza cika alkawuran da ya dauka yayin yakin neman zabe.

A wani faifan bidiyo da Legit ta samu ta gani, Mista Ibrahim, wanda ya fito daga Karamar Hukumar Jibia da ke cikin Jihar Katsina, ya ce yadda a da yake ganin kimar Buhari ya sa ya sanya wa ‘yarsa suna “Buhariyya ”.

Yace:

“A shekarar 2015, kwana 26 kacal kafin rantsar da Buhari, matata ta haifi diya mace. Na yi alkawari idan jaririn ya zama namiji, zan sanya masa suna Buhari kuma idan yarinya ce, Buhariyya. ”

Kara karanta wannan

Zan iya ziyartar Daura duk makonni biyu kuma babu wanda zai iya hana ni, Buhari

Sai dai ya ce sha'awar da yake yi wa shugaban a yanzu ta kau, saboda Buhari ya rasa kyakkyawar niyyar da yake da ita a da.

Dan Katsina ya yi bikin canza sunan diyarsa daga Buhariyya zuwa Kausar, ya ce Shugaban Kasar ya gaza
Dan Katsina ya yi bikin canza sunan diyarsa daga Buhariyya zuwa Kausar, ya ce Shugaban Kasar ya gaza Hoto: Katsina Post
Asali: Facebook

Mutumin ya kara da cewa:

“Duk wanda ya san ni ya san ina kaunar Buhari saboda Allah, domin kowa ya san mutumin kirki ne. A da can da an ambaci sunansa, kowa yana jin cewa shi ne mutumin da ya dace wanda zai iya taimakawa wajen magance matsalolinmu. Amma ya juye zuwa wani mutum na daban. ”

Buhari bai cika alkawurransa ko daya ba

A cewar Mista Ibrahim, shugaban bai cika ko daya daga cikin alkawuran yakin neman zabensa ba.

“Ina gaya muku, shugaban kasa bai fanshi daya daga cikin alkawuran yakin neman zabensa ba. Bai yi komai ba. ”

Ya ce yanzu ya fahimci cewa shugaban kasar ba zai iya cimma komai ba.

Kara karanta wannan

Shugaba Muhammadu Buhari ya koma Abuja bayan mako daya a Daura

Mista Ibrahim ya ce ya jinkirta shigar da ’yarsa a makaranta ne saboda shawarar da ya yanke na canza mata suna, don haka yanzu zai sanya Kauthar makarantar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel