Buhari ga 'yan siyasa: Kada ku yi amfani da ni wurin yaudarar masu saka kuri'a
- Shugaban kasan Najeriya yayi kira ga 'yan siyasa da kada su yi amfani da shi wurin yaudarar masu kada kuri'u
- Muhammadu Buhari ya yi kira ga masu tattara tarihi da su yi wa mulkinsa adalci wurin tattara nasarorinsa
- Ya kara da kira ga gwamnonin jam'iyyar APC da su jajirce wurin cikawa jama'a alkawurran da suka daukan musu
Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi kira ga 'yan siyasa da kada su yi wa mulkinsa karya domin samun hawa kujerun siyasa, Daily Nigerian ta ruwaito.
Shugaban kasan ya sanar da hakan ne a ranar Alhamis, yayin da ya karba bakuncin wasu gwamnonin da aka zaba karkashin jam'iyyar APC a Daura, jihar Katsina.
Kamar yadda Nigerian Tribune ta ruwaito, Buhari ya bukaci masu tattara tarihi da su yi adalci wurin ajiye tarihin mulkinsa, "ballantana wurin nunawa masu zabe da su yi zabi mai kyau na shugabanni a kasar nan."
KU KARANTA: Da duminsa: Kotu ta umarci DSS da su gabatar da mukarraban Igboho 12 da suka tsare
KU KARANTA: Da duminsa: Kotu a Kano ta haramtawa majalisar jiha binciken Rimingado
A wata takarda da babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Garba Shehu ya fitar, Buhari ya ce makomar kasar nan ta dogara ne ga jajircewa da kuma gaskiyar masu adana tarihi.
Shugaban kasa Muhammadu ya ce abun ba zai yi dadi ba idan aka batar da masu zabe da karairayi.
"A lokacin da ya rage da kuma wadanda ke da wa'adin mulki daya kamar yadda kundun tsarin mulki ya tanadar, zabuka manyan al'amura ne ga jam'iyyu.
“Masu rubuta tarihi ya dace su yi mana adalci ta yadda wadanda ke neman kujerun siyasa ba zasu yi amfani da rashin sanin jama'a ba wurin yaudarar su," yace.
Shugaban kasan ya umarci gwamnoni da su kasance masu jarumta da dagewa wurin cika alkawurran da suka yi wa jama'a.
"Mun yi iyakar kokarinmu kuma muna godiya ga Ubangiji kan abubuwan da muka samu muka yi," ya kara da cewa.
A wani labari na daban, Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal a jiya ya ce 'yan sa kai ne zasu jagoranci jami'an tsaro wurin yaki da miyagun 'yan bindiga a jihar.
Ya sanar da hakan ne yayin da sarakunan gargajiya na jihar suka kai gaisuwar sallah gidan gwamnatin jihar. Sarakunan sun samu jagorancin Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar.
Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, Gwamnan ya ce 'yan sa kan sun san dajin sosai kuma nan ne maboyar miyagun 'yan bindiga a jihar.
Asali: Legit.ng