An gano yaran makarantar Islamiyyar Tegina a yankin Shiroro
- Rahoto ya nuna cewa an gano yadda ’yan bindiga ke gararamba a daji da dalibai 136 da suka sace daga makarantar Islamiyyar Salihu Tanko da ke garin Tegina a Jihar Neja
- Sai dai uku daga cikin yaran sun mutu a hannun 'yan bindigar da suka yi garkuwa da su
- A halin yanzu, shugaban makarantar ya ce basu sake jin doriyar yaran ba tun bayan da suka biya wasu kudade
Rahotanni sun kawo cewa an gano dalibai 136 da aka sace a makarantar Islamiyya ta Salihu Tanko da ke Tegina, jihar Neja a yankin Lakpma na karamar hukumar Shiroro ta jihar.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa uku daga cikin yaran sun mutu a hannun masu garkuwar.
Tafidan Allawa, shugaban kungiyar matasan kungiyoyin Allawa, Jibrin Allawa, a wani sako da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, ya yi kira da a dauki kwararan matakan ceto yaran, yana mai cewa yanzu sun zama kamar masu cutar yunwa.
Ya ce:
“Akwai bukatar a dauki kwararan matakai wajen ceto yaran makarantar Islamiyyar Kagara da aka sace wadanda ke cikin Gandun Dajin Allawa..
“Mazauna yankin sun ja hankalinmu game da shige da ficen ‘yan fashin da ke dauke da daliban makarantar a kusa da yankin Lakpma na karamar hukumar Shiroro da yammacin Alhamis.
“Masu laifin sun tsallaka mahadar Maganda a kan titin Allawa pandogari, amma abin takaici, an kama wani mutum Jamilu Madaki Kurmi sannan aka harbe shi a hannu.
“Madaki ya tabbatar da ganin yaran makarantar Islamiyyar masu fama da rashin abinci mai gina jiki a kan babur din wadanda suka yi garkuwar da su.
“A ranar Lahadi da daddare, ‘yan bindigar sun afka wa kauyen Wutare sannan suka kame mutanen garin suna tilasta musu tsallakar da su kogin yayin da wasu mazauna kauyen suka ba da labarin mummunan halin da suka ga sauran yaran makarantar a matsayin abun tausayi.
"Bayan mun ji duk wadannan bayanan, mun tuntubi hukumomin da abin ya shafa amma abin takaici ba a dauki wani mataki a bayyane ba."
Ya yaba wa Matasan Shiro da ke kula da yadda suke kiyaye lamuran tsaro a koda yaushe tare da kusanto da hukumomin tsaro.
An biya fansa
A halin yanzu, shugaban makarantar, Malam Alhassan Garba Abubakar, ya shaida wa Daily Trust cewa iyayen daliban sun tara wasu yan kudade wanda aka mika wa yan fashin.
“Yanzu haka da nake magana da ku, babu wani sabon labari game da yaran.
“Lokaci na karshe da‘ yan bindigan suka tuntube mu shi ne kwanaki biyar da suka gabata kuma kafin lokacin mun sami damar tattara wani adadin daga cikin naira miliyan 30 din da suka nacewa wanda ba zan iya bayyana muku ba amma duk da kudin, ba su saki yaranmu ba.
“Sun gaya mana cewa uku daga cikinsu sun riga sun mutu kuma da irin wannan labarin babu iyayen da zai ji daidai. Mun yanke shawarar yin addu’o’i don neman taimakon Allah.”
Yan bindiga sun karbi N20m a matsayin kudin fansa, amma sun ki sako ’yan makarantar Neja
A baya mun ji cewa iyaye da ma masu fatan alheri da kuma mutane masu kishin addini sun ba da N20m a matsayin fansa ga ’yan bindigar da suka sace daliban makarantar Islamiyyar Salihu Tanko guda 156 a garin Tegina da ke Karamar Hukumar Rafi ta Jihar Neja wata daya da ta gabata.
Koda yake wani binciken jaridar THISDAY ya nuna cewa 'yan bindigar sun karbi N20million a matsayin kudin fansa a makon jiya amma sun ki sakin 'yan matan makarantar da ke hannunsu.
Asali: Legit.ng