Da duminsa: Matukin jirgin NAF ya sha da kyar yayin da 'yan bindiga suka harbo jirgi

Da duminsa: Matukin jirgin NAF ya sha da kyar yayin da 'yan bindiga suka harbo jirgi

  • Hatsabiban 'yan bindiga sun harbo jirgin yakin sama na dakarun sojin Najeriya a ranar Lahadi
  • Mai magana da yawun rundunar, Edward Gabkwet, ya ce matukin jirgin da dukkan wadanda ke ciki sun tsira
  • Ya sanar da yadda matukin jirgin yayi amfani da salon kwarewarsa wurin fita daga jirgin sannan ya samu mafaka a wani gari

Miyagun 'yan bindiga sun harbo jirgin sojin saman Najeriya a ranar Lahadi. An samu rahotannin faduwar jirgin saman sojojin amma sai hukumomi suka musanta.

Amma kuma a wata takardar da mai magana da yawun rundunar sojin saman, Edward Gabkwet ya fitar, ya ce an kaiwa jirgin saman farmaki ne yayin da yake dawowa daga wani aiki tsakanin iyakokin jihohin Zamfara da Kaduna.

KU KARANTA: Babu aikin da APC tayi da ta cancanci cigaba da mulki a 2023, Hanga

Da duminsa: Matukin jirgin NAF ya sha da kyar yayin da 'yan bindiga suka harbo jirgi
Da duminsa: Matukin jirgin NAF ya sha da kyar yayin da 'yan bindiga suka harbo jirgi. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Akwai bayyananniyar yarjejeniya cewa Buhari zai mika mulki ga Tinubu, Sanata Hanga

Kara karanta wannan

NAF: Rundunar sojin sama ta magantu kan labarin sabon hatsarin jirgin sama a Kaduna

Ya ce matukan jirgin da dukkan wadanda suke ciki an samu ceto su inda ya kara da cewa zakakurin matukin jirgin mai suna Flight Lieutenant Abayomi Dairo yayi nasarar fita daga jirgin.

Kamar yadda yace, "Ya yi amfani da kwarewarsa bayan tsananin ruwan wutan da yaji daga 'yan bindigan. A haka yayi kokari ya fita daga jirgin kuma ya samu mafaka a wani gari mafi kusa kafin safiya."

Legit.ng ta ruwaito yadda rundunar sojin saman Najeriya, NAF, ta musanta rahotannin dake yawo na hatsarin da jrigin samanta ya kara yi a Kaduna a ranar Lahadi da ta gabata.

Akwai rahotannin dake yawo na cewa jirgin sojojin saman Najeriya wanda ya taso daga jihar Adamawa ya fadi a wani wuri a cikin jihar Kaduna.

A wani labari na daban, a ranar Lahadi da ta gabata ne wasu fusatattun matasa suka bankawa wasu mutum 5 da ake zargin da garkuwa da mutane wuta a kan babbar hanyar Afuze-Ukoha dake karamar hukumar Owan ta yamma a jihar Edo.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: 'Yan bindiga sun kai hari sansanin 'yan sanda a Zamfara sun kashe 13

Kamar yadda TheCable ta ruwaito, wadanda ake zargin sun tare da sace wasu matafiya kan babbar hanya kuma sun kai su wani makusancin daji.

Amma kuma cike da sa'a ga matafiyan, masu garkuwa da mutanen sun shiga hannun 'yan sa kai wadanda suka fito dasu daga dajin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng