Yan bindiga sun karbi N20m a matsayin kudin fansa, amma sun ki sako ’yan makarantar Neja

Yan bindiga sun karbi N20m a matsayin kudin fansa, amma sun ki sako ’yan makarantar Neja

  • Barayin dajin sun karbi kudin fansar har N20m amma suka ki sakin daliban sannan ba su fadi dalilin hakan ba
  • Sai dai wata majiya ta ce N18m aka kai musu maimakon N20m
  • ’Yan mata 30 ne ke amfani da ledar taliyar spaghetti guda daya a zaman abinci

Yanzu haka an gano cewa iyaye da ma masu fatan alheri da kuma mutane masu kishin addini sun ba da N20m a matsayin fansa ga ’yan bindigar da suka sace daliban makarantar Islamiyyar Salihu Tanko guda 156 a garin Tegina da ke Karamar Hukumar Rafi ta Jihar Neja wata daya da ta gabata.

Koda yake wani binciken jaridar THISDAY ya nuna cewa 'yan bindigar sun karbi N20million a matsayin kudin fansa a makon jiya amma sun ki sakin 'yan matan makarantar da ke hannunsu.

Sai dai bayanin nan na zuwa ne bayan wadansu 'yan matan 'makarantar sun kubuta daga hannun barayin dajin wanda kawo yanzu adadin wadanda suka kubutan suka zama guda biyu cikin kwana hudu.

Bincike ya nuna cewa kwamitin da mai garin ya kafa ne ya kai kudin ga barayin amma bayan ‘yan fashin sun amshi kudin fansar, sunki sakin ’yan makarantar da suka sace.

makarantar Neja
Yan bindiga sun karbi N20m a matsayin kudin fansa, sun ki sako ’yan makarantar Neja
Asali: UGC

Wata majiya ta fada wa jaridar THISDAY cewa ‘yan fashin ba su bayar da dalilin da ya sa ba su sako ‘yan matan ba, amma wata majiyar ta ce ‘yan fashin ba su ji dadin yadda N18m kadai daga cikin N20m da suka bukata aka kai musu.

Majiyar ta kara da cewa ‘yan bindigar sun fada wa wadanda suka kai musu N18m din cewa kudin fansar ’yan mata 15 da suka tsere daga hannunsu a makon da ya gabata.

A lokacin da aka tuntube Shugaban makarantar, Alhaji Alhassan Abubakar, ya tabbatar da cewa da gaskiyar kai wa barayin dajin kudin fansar amma har zuwa lokacin da aka tuntube shi ya ce ’yan bindigar ba su sako 'yan matan ba.

Ya ce:

"Ba su ba da wani dalili ba da ya sa suka karbe kudin fansar amma suka ki sakin 'ya'yan namu."

Daya daga cikin daliban ta tsere

An samu labarin cewa Aisha Mohammed mai shekara 12 ta tsere daga hannun miyagun a ranar Talatar da ta gabata bayan ta yi ta gararamba a cikin daji na wuni biyu da dare guda.

Wata mata mai suna Zaynab Sale Boka ita ce yarinya ta farko da ta tsere daga hannun ‘yan fashin a ranar Litinin din da ta gabata.

Aisha ta fadawa jama’a bayan sun isa Tegina cewa sun yi shirin tserewa tare da wata yarinya amma sai dubunta ta cika.

Shugaban makarantar ya tabbatar da tserewar A’isha daga hannunn 'yan fashin, inda ta koka kan halin da sauran wadanda aka sacen ke rayuwa a hannun miyagun.

Ya ce, akalla 60 daga cikin 'yan matan suna fama da kumburin kafafu baya ga ramar da suke fama da ita saboda ’yan mata 30 na raba ledar taliyar spaghetti guda daya a matsayin abinci.

Ya roki jama'a da su taimaka wa iyayen domin ganin an sako ’yan matan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng